Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya amshi roƙon EFCC, inda ya amince su ƙwace gidajen tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu har guda 40.
A hukuncin wucin-gadi da alƙalin ya yanke a ranar Juma’a, ya ce ya bai wa EFCC umarnin riƙe gidajen, sannan kuma ta buga hotunan su a jaridu domin kowa ya gani.
Duk wanda ke iƙirarin na sa ne ba na Ekweremadu ba, to ya garzaya kotun domin ya kai hujjojin cewa shi ya mallake su.
Cikin 2022 ne EFCC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya, inda ta shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1242/2022, inda ta nemi kotun ta ba ta iznin riƙe gidajen da ta ke zargin na Ikweremadu ne, kafin a kammala shari’a.
EFCC ta yi zargin cewa da kuɗaɗen talakawa ya sayi gidajen, kuma hakan ya nuna cewa an karya Dokar Hana Zamba ta Sashe na 17, ta 2006.
An ɗage shari’ar zuwa 5 Ga Disamba. Idan har aka kasa samun wanda ya fito ya bayar da gamsasshiyar shaidar gidajen sa ne ba na Ekweremadu ba, to a ƙarshe kotu za ta ƙwace gidajen ɗungurugum, ta damƙa wa Gwamnatin Tarayya.
Daga ciki gidaje da maka-makan filayen 40, akwai 10 a Enugu, 15 a Abuja, 1 a Legas, 2 a Ingila, 3 a Amurka, 9 a Dubai.
A halin yanzu dai Ekweremadu na Ingila a tsare a kurkuku, tun bayan kama shi da aka yi ya je dashen ƙodar wata ɗiyar sa ba bisa ƙa’ida ba.
An sake shi da laifin tafiya da wani ƙaramin yaron da za a cire ta sa ƙodar ɗaya a dasa wa ‘yar Ekweremadu ɗin
Discussion about this post