Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwana! Ku sani, lallai idan al’ummah ta rasa shugabanni nagari to matsala ba zata taba karewa a cikin wannan al’ummar ba. Don haka kenan ya zama tilas, dole kuma wajibi kowanenmu ya tashi tsaye, domin ya bayar da gudummawa wurin tabbatar da shugabanci nagari a wannan kasa tamu mai albarka. Domin idan mun samu shugabanci nagari, to da ikon Allah kowa zai amfana, kuma da yardar Allah kowa zai ji dadi, kasancewar shugaba nagari rumfa ce wurin hutawa ga bayin Allah.
Lallai lokaci ya wuce da zamu rungume hannuwa, muce mu babu ruwan mu da lamarin wadanda suke shugabantar mu; har ga Allah wannan bai dace ba, babban kuskure ne, kuma sam ba dabi’a bace ta mutanen kirki. Domin idan muka ce haka, har aka wayi gari ashararan mutane, ‘yan iska, ‘yan tasha, ‘yan daba, ‘yan gareji, marasa mutunci suka shugabancemu, kuma ya zamanto sune suke mulkar mu, to lallai mun gama yawo, sai buzun mu, kuma wallahi kashin mu ya bushe, kuma sai wasu bamu ba.
Muna dai ji, kuma muna gani, irin yadda wasu da ake kira shugabanni, maimakon su samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da walwala cikin al’ummah, sai aka wayi gari suna kokarin tunzura jama’ah, su tayar da hankula ta hanyar fadar wasu maganganu da basu dace ba, irin na ‘yan daba, kamar kalmar koda-tsiya-koda-tsiya-tsiya, da sauran su. Jama’ah wallahi irin wadannan mutane kuskure ne ace an bar su, an zuba masu ido suna shugabancin mutane yadda suka ga dama.
Ta yaya za’a kawar da ire-iren wadannan miyagun mutane daga lamarin shugabanci a kasar nan? Wannan zai faru ne idan kowannen mu ya taka rawar da ya kamata ya taka, wurin tabbatar da shugabanci nagari.
Ya ku jama’ah! Ina kiran ku baki daya da cewa kar kuji tsoron kowa sai Allah. Kar kuji tsoron barazanar duk wani mai barazana. Kar ku yarda wani mutum ya zare maku ido, kar ku yarda a yaudare ku ko a ha’ince ku. Ku tsaya tsayin daka, ku tabbatar da cewa tilas sai anyi abunda ya dace.
Wulakancin ya isa haka nan. Cin mutuncin ya isa haka nan. Rainin wayon ya isa haka nan. Kar mu yarda da duk wani mayaudari ko maha’inci, kuma wallahi koda da sunan addini yazo, muce bamu yarda ba, muce ba zamu amince ba. Mu sani, babban masoyinmu, jagoranmu, Annabi Muhammad (SAW), yace:
“Ba’a cizon mumini har sau biyu a rami daya.”
Lallai bai kamata mu zama wawaye ba, bai kamata mu zama gidadawa ba, bai kamata mu zama kidahumai, har mu sake bari ayi wasa da hankalin mu ba. Bai kamata mu sake bari a cuce mu ko a yaudare mu ba.
Gaskiyar magana shine, yaudarar ta isa haka nan!
Wallahi ya zama dole, tilas kuma wajibi mu tashi tsaye, mu hada karfi, mu hada karfi da karfe, mu bayar da gudummawa wurin samar da shugabanci nagari, shugabanci na adalci, wanda kowa zai ji dadinsa da karfin ikon Allah da kuma yardar sa, da amincewarsa.
Babu saurarawa, babu daga kafa, babu tsoro, kuma babu-gudu-babu-ja-da-baya.
Kar muji tsoron duk wani shedani, kar muji tsoron duk wani dan daba, kar muyi shakkar kowa. Domin idan babu shugabanci nagari, wallahi kowa zai ji a jikinsa, zai shafi kowa.
Idan babu shugabanci nagari ba za’a samu zaman lafiya ba, ba za’a samu kwanciyar hankali ba, ba za’a samu ci gaban tattalin arziki ba, ba za’a samu hadin kai da kaunar juna ba, kai wallahi ko addini ba za’a samu damar yin sa daidai ba.
Sai dan Adam ya samu natsuwa, zaman lafiya da kwanciyar hankali sannan zai samu damar bauta wa Allah shi kadai, ba tare da ya hada shi da kowa wurin bauta ba.
Lallai ne duk wanda yayi muna ta’addanci, muma muyi masa ta’addanci gwargwadon yadda yayi muna ta’addanci. A wannan karon kar mu yarda da duk wani shashanci. Wajibi ne mu sadaukar da rayukanmu domin ceton rayukanmu da rayukan ‘ya ‘yanmu da jikokinmu. Dole ne mu tashi tsaye domin mu kare mutuncinmu da mutuncin al’ummarmu.
Kar mu sake saurara wa duk wani da yake son rusa mu da bata muna rayuwa.
Bayin Allah masu girma! Lallai tabbas, ko shakka babu yana daga cikin hanyoyin samar da zaman lafiya a cikin al’ummah, da dorewar farin cikin mutane, a samar da shugaba nagari, adali, mai kamanta gaskiya da adalci, marar nuna banbanci da nuna kabilanci tsakanin ‘yan kasa, kuma mai ingantacciyar lafiya. Wanda yake son mu muma muke son sa. Wanda yake yi muna addu’a muma muke yi masa addu’a. Domin da samun natsuwa ne kadai mutane zasu samu damar yin ita kan ta bautar Allah cikin walwala, aminci da jin dadi.
Wasu daga cikin mutane har yanzu hankalin su yaki kwanciya, sun kasa daidaita tunaninsu wuri daya, ta yadda zasu fahimci amfanin shugabanci da muhimmancinsa a cikin al’ummah. Wasu sunyi wa al’amarin shugabanci mummunar fahimta, shi yasa suke ta kokarin gudu daga bayar da gudummawa wurin samar wa al’ummah shugaba nagari.
Wani lokaci laifin yana kan talakawa ne, ta yadda suke bin son zuciyarsu. Saboda kwadayin abun duniya, sai su zaba tare da dora mutanen banza akan shugabancin al’ummah, wato su dora wadanda su kan su sun san basu cancanta ba. Kuma wannan ya samo asali ne idan mutanen kirki suka guji siyasa, suka kyamace ta, wai saboda karya, yaudara, ha’inci da cin amana sunyi yawa a cikin ta.
Watakila da ace sun shiga lamarin da mutanen banza da ke ciki sun kauce daga cikinta, saboda siyasa a Musulunci tana da mutukar amfani da fa’ida.
Don haka ina kira a gare mu baki daya, da mu zo mu fahimci menene girma da matsayin shugabanci, wannan ne zai sa mu zabi shugaba nagari, adali wanda zai kiyaye muna lamurran harkokin duniyar mu da kuma lahirar mu.
Jagorancin al’ummah da kula da lamarin su, da jawo alkhairi zuwa ga re su, da tunkude masu sharri, tare da kokarin gyara masu duniyarsu da lahirarsu shine ake nufi da siyasa ba wani abu ba.
Koda yake kada mu manta da yadda wasu suke amfani da wannan kalmar da ma’anar yaudara, ko kuma a sanya bangaranci a cikin warware wasu al’amurra, ko kuma a kushe wani abu da ya fito ba daga bangaren mu ba, da makamantan hakan.
A duk lokacin da muka fito muna maganar a zabi shugaba nagari, adali, mai kamanta gaskiya da adalci sai wadanda basu fahimci abinda ake nufi ba, su koma gefe suna surutan banza da zage-zage da guna-guni, suna cewa siyasa ba addini bace, ko kuma babu ruwan addini da siyasa. Irin wadannan mutane, da sun san me ake nufi da siyasa da basu fadi haka ba, saboda idan mun duba tarihin rayuwar dan Adam tun farkon samuwarsa, ai yana tare ne da siyasa.
Saboda haka don Allah mu dawo da hankulan mu wuri daya, mu dubi fadin Allah cewa:
“Ni mai sanya Khalifah ne (mai wakilta ta) a bayan kasa…” [Suratul Bakarah: 30]
Da fadin Allah cewa:
“Ya kai Dawuda mu mun sanya ka Khalifah (mai wakiltar Allah
cikin tafiyar da al’amuran bayi) a bayan kasa, sai ka yi hukunci tsakanin mutane da adalci…” [Suratul Sad: 26]
Don haka mu tsaya tsaf don mu zabi shugaba nagari, adali, wanda zai kula da hakkokan mu.
Ya zama wajibi mu duba mutum mai lafiya, mai ilimi, mai kamala, mai kyakkyawar manufa, mai kamun kai, mai nisantar miyagun dabi’u wadanda suke zubar da kimar mutum a cikin al’ummah, misali: shaye-shaye, neman mata, fadace-fadace, zage-zage, kabilanci da cin hanci da rashawa.
Haka kuma shi shugaba nagari yana da manufa mai kyawo akan al’ummah. Za’a fahimci hakan ne ta hanyar duba da irin yanayin rayuwarsa a cikin mutane, da karfin tausayi da yake da shi, da inda yasa gaba a cikin sha’aninsa, ta fuskar addini; shin zai taimaki addini, shin zai taimaki bayin Allah wadanda Allah yace a taimaka masu; irin marayu, musakai, fakirai da sauran su.
Abun mamaki, yau sai kaji mutum yazo yana kamfen, yana kiran zan yi maku abu kaza da kaza, amma har ya gama jawabinsa, babu maganar taimako ga mabukata, babu maganar taimakon addini, babu maganar inganta rayuwar al’ummah, kawai sai buge-buge da kame-kame. Allah ya kyauta, amin.
Shugaba nagari shine wanda zai yi kokari yaga cewa ya gina mulkinsa akan tsoron Allah, da bin dokokin Allah, da bin dokokin kasa, tare da tabbatar da hukunta duk wanda ya taka doka. Kuma dole ne shi kan sa shugaban ya zamo mai bin doka da oda. Yin hakan zai bayar da tabbacin hukunta duk wanda ya karya dokar. Amma misali, shugaba yace abar kaza da kaza, amma kuma sai a wayi gari shine a gaba wurin aikata abun, wannan shirme kenan.
Sannan dole ne shugaba ya kasance mai kyakkyawan tunani, mai natsuwa da hangen nesa, wato yasan abinda zai je ya dawo. Duk lokacin da aka wayi gari shugaba bai da natsuwa, to babu ko shakka mulkinsa zai kare ne a birkice. Mu sani, komai yana bukatar tunani, natsuwa da hangen nesa, domin dora komai akan muhallinsa da ya dace. Hakan yana nuni da cewa tilas shugaba ya zamo yana da baiwa ta hangen nesa, ta yadda zai ciyar da al’ummarsa gaba. Kuma hakan baya tabbatuwa sai da ilimin addini dana zamani.
Amma kawai don dibgewa da anga mutum ya tara kudi, shike nan sai ace shine jagora, koda kuwa bai san komai ba. To don Allah ta yaya tunani mai kyau zai kasance ga mutumin da yake jahili, wanda komai zai aikata a kuskure zai yi?
Sannan dole shugaba ya kasance mai bin lamari da sauki. Kar ya kasance mai tsatstsauran ra’ayi, ko mai akidar ra’ayin rikau, musamman idan ya zamanto ba akan gaskiya ba, amma idan akan gaskiya ne, to anan aka fi son ya zama mai ra’ayin rikau.
Tsatstsauran ra’ayi ko ra’ayin rikau yana nufin shugaba ya yanke hukunci da tunaninsa shi kadai, kuma koda tunanin nasa ya kasance baya kan hanya. Irin wannan ra’ayi shi yake haifar da mulkin kama karya, mulkin da talaka bai da ‘yancin ya bayyana kukansa.
Sannan dole ne shugaba ya girmama karfin mulki, saboda idan ya girmama mulkin sai a girmama shi, idan ya tozarta mulkin sai a tozarta shi cikin sauki.
Yaku ‘yan uwa, sannan mu sani cewa duk shugaban da yake girmama matsayin sauran ma’aikatan dake aiki a karkashinsa, ko karkashin gwamnatinsa, to wannan shugaba shugaba ne nagari. Hakan yana nufin zai iya baiwa kowa hakkin aikinsa da daraja, daidai da yadda karfin doka ta ba shi.
Misali, zaka ga wani shugaba yana wulakanci da cin fuska, musamman ga nakasa da shi.
Bayin Allah nagari! Ga wadansu muhimman halaye a takaice, wadanda ya zama wajibi kowane shugaba daga sama har ƙasa ya sifantu da su:
1. Dole shugaba ya zamo adali. Adalci shine tushen samun nasarar kowane irin shugabanci. Adalcin Allah Ta’ala shine yake riƙe da sammai da ƙassai. Dole ne shugaba yayi adalci ga duk wanda yake ƙarƙashinsa, ya bai wa kowa haƙƙinsa, ba tare da nuna wani bambanci ba. Amr Ibnul As (RA) yana cewa:
“Mulki ba ya yiwuwa sai da tsayayyun jami’ai, su kuma ba zasu samu ba sai da kuɗi, kuɗi kuma ba su samuwa sai ana raya ƙasa, raya ƙasa ba ya yiwuwa sai da adalci. Kuma yana daga cikin adalci shugaba ya hana azzalumai yin zalunci, ya hana maɓarnata yin ɓarna, kai kada ma ya bari har sai talakawa sun fara kokawa, saboda in har aka kai matsayin da suka fara kokawa to zasu iya ɗaukar doka a hannunsu.”
2. Lallai ne shugaba ya kasance mai nisantar zubar da jinin mutane. Kar yayi kar ya bari ayi.
3. Dole ne shugaba ya kasance mai magana ɗaya, babu ƙarya babu yaudara, babu ha’inci.
4. Dole ne shugaba ya zauna da mutanen kirki masu tsoron Allah; kada ya saki fuska ga azzalumai da ashararai, kada su samu sakewa a ƙarƙashin ikonsa.
5. Dole shugaba ya kasance mai cika alƙawari, mai faɗar gaskiya. Idan yasan ba zai yi ba; kar yace zai yi, kar kuma bai yi ba yace yayi.
6. Kar shugaba ya raina abokin gaba komai rauninsa.
7. Lallai ne shugaba ya samu likita na musamman, ƙwararre mai amana, masoyi na haƙiƙa; kuma kada ya dogara da likita guda ɗaya, a’a ya sami wadatattun likitoci waɗanda in wani gagarumin ciwo ya same shi za su haɗu a kansa. Idan bakinsu yazo ɗaya akan irin maganin da za’ayi masa to sai ayi, bayan shawartar waɗansu amintattunsa keɓaɓɓu.
8. Dole ne shugaba ya bai wa mataimakinsa muhimmanci sosai. Kar ya ture shi gefe guda, ta yadda zai zama kamar ɗan kallo a harkar mulki; amma kuma kada ya yarda ya bari har ya sake, ya miƙe ƙafa har yafi shi ƙarfi ya zama kamar shine shugaban shi kuma ya zama hoto.
9. Haka kuma dole ne shugaba ya samar da kyakkyawar jituwa, da kyakkyawar alaka tsakaninsa da ‘yan majalisarsa, ya rinka zama dasu akai-akai yana shawartarsu, wato kowa yaji cewa ana yi da shi; kowa yasan cewa babu ɗan mowa da dan bora a cikinsu; sannan kuma babu waɗansu fulogai waɗanda su kaɗai ne suke jan mai, kuma idan babu su babu inda za’a je. Wannan zai haifarwa da shugaba babbar matsala.
10. Dole shugaba ya kula da tattalin arziƙin kasa sosai, musamman sana’o’i da harkokin kasuwanci. Dole ya buɗawa mutane hanyoyin samun arziƙi da ayukkan yi, musamman ga matasa; dole ne ya rinka tallafawa ‘yan kasuwa, sannan kada ya ɗora masu haraji mai yawa, ko ya basu bashi da kuɗin ruwa. Kuma lallai ne shugaba ya kiyayi abin hannun mabiyansa. Ya guji karɓe-karɓe da cushe-cushe, da karbar cin hanci da rashawa, ko karbar daloli da nairori yana zuba wa aljihu.
11. Dole ne shugaba ya kasance mai tattali da tsimi da tanadi da shirin ko-ta-kwana; musamman tanadin abinci da kayan masarufi, saboda bayar da agajin gaggawa a lokacin da wata musiba ta afkawa kasa kwatsam; yadda ba sai an fita waje da ƙoƙon bara ba.
12. Dole ne shugaba ya kasance mai cika alƙawari, yayi kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya taimaka masa; musamman a lokacin da yake neman mulki. Kar mutane su tura mota ta tashi ta bar su da hayaƙi.
13. Kar shugaba ya bari wani talaka ya san wurin hutunsa da shaƙatawarsa, ballantana har yaje wurin; wannan zai janyo raini, abokan mu’amalar gudanar da mulki kaɗai zai bari su rinka halartar irin wannan wurin idan ya buƙaci zuwansu, domin tattauna muhimman al’amurra cikin nutsuwa.
14. Dole ne shugaba yayi ƙoƙari ya guji aikata duk wani abin da zai jawo masa baƙin jini da maƙiya.
15. Kada shugaba ya naɗa ‘yan uwansa a manyan muƙamai, saboda gudun hassadar ‘yan uwa. Amma ya kai matuƙa wurin kyautata masu da mutunta su; sannan kuma yasa ido a kansu yayi kaffa-kaffa da su, yayi haƙuri kan cutarwarsu.
16. Lallai ne shugaba yayi kokari ya kula da halaye guda uku, kuma ya rike su: 1. kyauta 2. Haƙuri 3. Da tabbatar da gaskiyar komai kafin ya ɗau mataki a kan sa.
17. Dole shugaba ya rinka yabo da zargi daidai ƙurji daidai ruwa. Wato kar yayi yabo fiye da ƙima, kuma kar yayi ta zargi, faɗa, ko mita fiye da ƙima. Haka kuma ya daidaita tsakanin alƙawarukkansa da barazanarsa. Kada barazana tafi yawa, kada kuma alƙawari yafi rinjaye.
18. Shugaba ya kasance mai halin ba-sani-ba-sabo, duk wanda ya taka doka, doka ta taka shi.
19. Dole ne shugaba yasan cewa abubuwa uku sune suke tabbatar da nagartar kowane mulki; 1. Darajanta, kimanta da daukaka da inganta addinin mutane. 2. Tabbatar da tsaro da zaman lafiya. 3. Inganta rayuwar al’ummah.
20. Kar shugaba ya zama mai nuna kabilanci, da fifita wasu akan wasu, da nuna bambamce-bambamce tsakanin ‘yan kasa.
Daga karshe, Wallahi ya sama wajibi mu sani, duk wanda ya bayar da gudummawa ko wace iri ce, domin a dora wa al’ummah rubabben shugaba, wanda bai dace ba, to lallai tun anan duniya zai fara ganin munin sakamakon aikinsa, kafin ya tafi lahira kuma, yayi tanadin irin amsar da zai bai wa Allah, Mahaliccinmu!
Sannan duk wanda ya rungume hannu, yaki ya bayar da gudummawa ko wace iri ce, domin samar wa al’ummah shugaba nagari, shima ya tanadi irin amsar da zai ba wa Allah gobe alkiyama, bayan yasha wahala anan duniya, sakamakon mummunan aikinsa!
Allah Subhanahu wa Ta’ala ya hore wa kasar nan arzikin da kowa zai amfana, amma saboda miyagun halayen mu da rashin shugabanci nagari, sai aka wayi gari muna ta shan wahala!
Wassalamu Alaikum
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post