Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun kashe wani hatsabibin ɗan bindiga dake kira da Kachalla Gudau a Kaduna.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce ” Gudau ne shugaban ‘ya ta’adda da suka addabu mutane da kisa da yin garkuwa da mutane a kananan hukumomin Chikun, Kachia da Kajuru.
Sojoji sun gama da shi ranar Lahadin wannan mako a harin da suka kai cikin ƙurgurmin dajin dake Kaduna yankin inda nan ne maɓoyar sa.
“Majiya mai tushe ta bayyana cewa Gudau na daga cikin ‘yan ta’addan da suka ji raunin harsashi a lokacin da sojoji sufa fatattake su da ruwan harsasai a wannan rana.
Sai dai da yake ba zai iya gudu ba saboda zafin harsashi da ya huda shi jami’an tsaro sun kama shi kuma a hannun su ya cika.
Gudau dan bindiga ne da ya shahara a wajen yin garkuwa da mutane musamman dalibai a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia.
Gudau na kashe mutanen da ya yi garkuwa da su musamman idan suka nemi arcewa daga wurin sa a daji sannan kuma kasurgumin barawon shanu ne da kuma safara muggan kwayoyi.
“Gudau bai bar kowa ba, ya kan kai wa Fulani hari a rugagensu, idan ya tarwatsasu sai ya kwashe musu shanu da dabbobi ya yi gaba da su.
Discussion about this post