Shugaba Muhammadu Buhari ya garzaya Landan babban birnin Ingila domin ganin likitocin sa. Zai kwashe makonni biyu kafin ya dawo gida Najeriya.
Buhari ya garzaya ne ana kwanaki ɗaya tal kafin ranar da aka tsara zai kai buɗe Taron Makon Masu Haƙar Ma’adinai a Abuja, domin a nuna wa masu zuba jari cewa Abuja ba ta da wata matsalar barazanar tsaro.
Ofishin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa ya fitar da sanarwar cewa “Shugaban Ƙasa ta tafi Ingila domin a duba lafiyar sa kamar yadda akan yi akai-akai. Kuma zai yi makonni biyu a can kafin ya dawo.”
Buhari ya tafi Landan ne kwanaki kaɗan bayan dawowar sa daga Koriya ta Kudu.
“Shugaba Buhari ya tafi Landan a ranar 31 Ga Disamba, 2022. Zai je a duba lafiyar sa kamar yadda ya kan je ana duba shi a kai a kai. Sai cikin mako na biyu na watan Nuwamba zai dawo,” haka Kakakin Yaɗa Labaran Buhari, Femi Adesina ya bayyana a sanarwar da ya fitar a shafin tiwita, ranar Litinin da rana.
Tafiyar da ita kan ta sanarwar bazatar sun jefa damuwa a zukatan mutane da dama, har su na cewa ta yaya Buhari zai fasa halartar taron Makon Masu Haƙar Ma’adinai da za a fara ranar Talata.
An shirya taron ne domin a jawo hankalin masu zuba jari, masu ilmi da ƙwararru a ɓangaren inganta masana’antu, a taron wanda za a yi a International Conference Centre, Abuja.
“Domin tabbatar da cewa Abuja na zaune lafiya babu wata barazanar tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari ne da kan sa zai buɗe taron.”. Haka Ministan Ma’adinai, Olamilekan Adegbite ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi.
Buhari ya bar Najeriya lokacin da ake ta dambarwar batun canja launin takardun naira, lamarin da Buhari ya ce shiri ne mai kyau.
Tun bayan hawan sa mulki ya ke yawan zuwa Ingila ana duba lafiyar sa. Akwai ma lokacin ya yi kwanaki 200 a Ingila ya na jiyya.
Discussion about this post