Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar IPOB sun kashe sarkin Obudi Agwa, Ignatius Asor a jihar Imo.
Maharan sun dira fadar sarkin dake kauyen Agwa a karamar hukumar Oguta da misalin karfe 12:30 na ranar Litini.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Michael Abattam ya sanar da haka a garin Owerri.
Abattam ya ce maharan sun afka fadar ne bayan sun badda kama, sun yi shigan masakai suna koke koke suna kira da a taimake su. Da suka kai gaban sarki sai suka ciro bindigogin sa dake ɗaure a bayan su suka ɗirka wa sarki da wasu hadiman sa dake tare da shi.
Abattam ya ce bayan sun fara ce daga gidan sarkin sai suka ɗunguma ofishin ‘yan bindiga garin, a nan ma suka kashe wani mutum ɗaya.
Kwamishinan’yan sandan jihar Ahmed Barde ya yi kira ga mutanen kauyen da su kwantar da hankalinsu domin rundunar za ta gudanar da bincike domin kamo maharan.
Discussion about this post