Babban Kwamandan Kula da Jiragen Yaƙin Iran, ya bayyana cewa ƙasar sa ta ƙirƙiro wani sabon samfurin makami mai linzamin da babu wata ƙasa mai wani makamin da zai iya kakkaɓo shi, ballantana ya hana shi kaiwa inda zai yi ɓarna.
Amir-Ali Hajizadeh ya bayyana kamar yadda Iran Press TV ta wallafa cewa kafin a samu wata ƙasar da za ta iya yin fasahar ƙirƙiro makamin da zai zama rigakafin hana makamin Iran yin ɓarna, to sai dai ko bayan nan da shekaru goma.
Hajizadeh, wanda kuma har shi babban jami’i ne Zaratan Sojojin ‘Republic Guard’ na Iran, ya ce makamin zai iya keta ƙasa, sama kuma duk wani makamin kakkaɓo makami mai linzami, idan ya ci karo da sabon makamin Iran, tarwatsa shi.
Iran ta ƙirƙiro wannan makami a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da samun saɓani tsakanin ta da Amurka da ƙasashen Turai dalilin yaƙin da ta ke yi da Ukraniya.
Discussion about this post