Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana cewa hukumar sa na buƙatar ƙarin karnukan da ke sinsino muggan ƙwayoyi, duk kuwa da cewa tsadar kowane ɗaya ta kai Dala 20,000.
Marwa, wanda tsohon Burgediya General ne, ya yi wannan ƙarin bayani a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, mai kula da harkokin ƙwayoyi.
Shugaban Kwamitin Harkokin Ƙwaya, Francis Agbo ne ya nusar da Marwa cewa ya fahimci kamar babu irin karnukan da ke sinsinar muggan ƙwayoyi a Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikwe, Abuja.
Marwa ya amsa da cewa ba zai bayyana cewa akwai ko babu ba, kuma ba zai bayyana wa kwamitin adadin yawan karnukan da ake da su ba, saboda dalilai na tsaro.
Amma dai ya ce na’ura mai gani har hanji da aka sa a filin jirgin, ba za ta taɓa barin a shigo da muggan ƙwayoyi ba tare da ta fallasa ba.
Ya ce ‘Yan Sandan Bincike na Jamus sun yi ƙoƙari sosai inda su ka bayar da karnukan ga Najeriya.
“Kuma yanzu haka su na makarantar horaswa da sarrafa karen bankaɗo kayan laifi a Legas. Ya ce makarantar za ta riƙa bayar da horo ga jami’an tsaro na ƙasashen Afrika ta Yamma.
Da ya ke magana kan nasarori, Marwa ya ce cikin watanni 20 NDLEA ta kama muggan ƙwayoyin da kuɗin su ya kai Naira biliyan 420.
Daga nan ya roƙi kwamitin ya sa a ƙara wa kasafin gina gidajen jami’an NDLEA, daga Naira biliyan 13 zuwa biliyan 23.
Shugaban Majalisar ya ce za su tabbatar NDLEA ta samu ƙarin kuɗaɗen.
Discussion about this post