Gwamnatin Tarayya ta amince ta ƙirƙiro sabon Tsarin Koyarwa da Harshen Gida (NLP), wanda idan an fara amfani da shi, za a riƙa koyar da yara ‘yan aji 1 zuwa 6 na firamare da yaren da su ke ji.
Gwamnatin Tarayya ta amince da wannan tsari ne a Taron Majalisar Zartaswa na yau Laraba, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar sa.
Ministan Harkokin Ilimi, Adamu Adamu ne ya sanar da shigo da wannan sabon tsarin, yayin da ya ke hira da manema labarai, a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga taron.
Sai dai ya ce a yanzu an amince ne kawai da tsarin, sai nan gaba za a fara aiwatar da shi, bayan an yi masa dukkan shirye-shiryen da su ka wajaba a tanadar masa.
Ya ce sai an tsara manhaja, an horas da malamai, kuma an zayyana yadda fasalin darussan za su kasance, tun daga kan ‘yan aji 1 har zuwa kan aji 6 na firamare.
Da ya ke jaddada cewa akwai buƙatar lokaci kafin a fara koyarwa a bisa wannan sabon tsarin, Minista Adamu ya ce “akwai yaruka har 625 da Najeriya, kuma ana so kowane yare a ba shi haƙƙin sa, a riƙa koyar da yara masu jin yaren da harshen su.
Ya ce a duk al’ummar da makaranta ta ke, to da yaren jama’ar da ke wurin za a riƙa koyar da su.