Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bayyana cewa ya tanadi hanyoyi, tsare-tsare da matakan da za su hana mazauna yankunan karkara tagayyara ko jigata saboda neman canjin sabbin kuɗi.
Cikin wata sanarwa Babban Bankin Najeriya ɗin ya fitar a makon jiya, an bayyana cewa kowa ya kwantar da hankalin sa, sauyin launin kuɗin ba zai hargitsa jama’a ko ya sa su cikin halin ƙunci ba.
Tun bayan da aka yi sanarwar sauya launin kuɗi ne jama’a da dama ke nuna damuwa dangane da aka bayar da wa’adin watanni uku, zuwa 31 Ga Janairu za a daina amfani da tsoffin da ake tasarifin su a yanzu.
CBN ya ce tun daga ranar 15 Ga Disamba za a fara kashe sabbin kuɗi.
A kan haka ne CBN ya ce ya tuntuɓi dukkan ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki su tabbatar sauyin launin kuɗaɗe bai wahalar da mutanen karkara ba ”
Ya ce dukkan hedikwatar CBN 36 da ke faɗin ƙasar nan za a yi amfani da su wajen biya wa jama’ar karkara buƙatar sauya kuɗaɗe.
CBN ya samu amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ya sauya lauyin kuɗi domin daƙile tsadar kayan masarufi da ƙuncin rayuwa.
Haka nan kuma za a sauya launin kuɗaɗen domin a rage yawan kuɗaɗen da ke hannun jama’a ba a juya su, sai kuma yawan kuɗaɗen jabu da ake bugawa, waɗanda dukkan su matsaloli ne ga tattalin arzikin ƙasa.
Discussion about this post