Bayanai da dalilai na ci gaba da fitowa fili dangane da abin da ya tunzira matasa a Jos yin jefa da tayar da ƙura wurin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
APC ta ƙaddamar da yaƙin zaɓen ɗan takarar ta Bola Tinubu da mataimakin takarar sa Kashim Shettima a Jos, babban birnin Jihar Filato a ranar Talata.
Cikin waɗanda su ka halarci fara kamfen ɗin har da Shugaba Muhammadu Buhari. Sannan kuma Filato can ne jihar Babban Daraktan Kamfen ɗin TInubu da Shettima, wato Simon Lalong.
Sai dai kuma taron ya haɗu da cikas, yayin da wani dandazon matasa suka tayar da rincimi a wurin taron.
Wani bidiyo da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya, ya nuna yadda matasan ke antaya jifa, yayin da mai gabatarwa ke ta magiyar ba su haƙuri, ya na cewa:
“Mai ƙaunar Allah da Annabi ya daina. Don Allah ku daina. Jami’an tsaro don Allah ku yi haƙuri ku daina dukan mutanen nan. Don Allah ku yi haƙuri.”
Mai gabatarwa ya riƙa maimaitawa kisan sau 15, amma yaran ba su daina ba.
Gangamin APC A Jos: Yadda ruwan ƙuri’un 2015 da 2019 ya janyo wa APC jifa a Jos:
Wani bidiyo da aka yaɗa a shafin sada zumunta na TikTok, kuma PREMIUM TIMES Hausa ta mallaki bidiyon, an nuno wani mutum mai kimanin shekaru 35 ya na magana a fusace, ya na bayyana ƙorafin da su ke da shi a kan jam’iyyar APC.
Matashin dai bisa alama ya na magana ne da yawun ‘yan Karamar Hukumar Jos ta Arewa, inda ya ke cewa:
“Wallahi mu Jasawa ba mu da dalilin da za mu fito mu na ihwe-ihwen banza. Banda Ƙaramar Hukumar Kano Municipal, babu inda aka ba Buhari ƙuri’u masu yawa a 2015 da 2019 kamar Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Amma ba abin da ya yi mana. Ko ambasada bai ba mu ba. Amma ‘Yar’Adua da ba mu zaɓe shi ba, ya ba mu har Minista. A je a duba a gani.Ba abin da Buhari ya yi mana. Ba gyaran da ya yi. Shi ma Gwamna Lalong bai yi mana komai ba.”
PREMIUM TIMES Hausa ta bi diddigin ƙuri’un da Jos ta Arewa su ka jefa wa APC a zaɓen 2015 da 2019.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2015, Jos ta Arewa ta zuba wa APC ƙuri’u 95,800, yayin da PDP ta samu 53,277.
A zaɓen 2019 kuma APC ta samu ƙuri’u 106,526, ita kuma PDP ta samu 25,574 a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, ƙuri’un da APC ba ta samu kamar su a kowace ƙaramar hukumar ƙasar nan 774 ba.
Discussion about this post