LƳan Najeriya daga ɓangarori da dama sun tofa albarkacin bakunan su game da tsare ɗalibi Aminu Mohammed da uwargidan shugaban kasa ta sa aka tsare ta kuma sa aka rika ratattaka masa duka a gabanta saboda wani rubutu da yayi ya saka hotonta.
Waɗanda suka zanta da PREMIUM TIMES HAUSA sun yi tir da tsare Aminu da SSS suka yi suna masu yin kira ga Aisha Buhari ta wa Allah ta sa a saki wannan matashi.
Zainab Ali ta ce ” Ni dai mace ce kuma uwa, amma ba komai bane za a ce yaro ya faɗi a kan ka ka ɗau irin wannan mataki. Idan bai yi maka daɗi ba sai ka nemi iyayen sa da wasu ma gaba su sanar da su. Amma a ganina irin abinda ya rubuta, bai kai ace kamar matar shugaban kasa ta yi wani abu a kai ba.
Bala Kasimu ” Ni fa wannan abu da aka yi wa wannan matashi ya sa ta sire min. Da ina mata ganin mace ce mai tausayi, amma wallahi ba ta yi masa adalci ba. A wannan zamani na yanar gizo me nene ba a cewa. Da dai ta nuna dattaku ta hakura da ya fi mata.
” Ni a nawa ganin kawai don ɗan Arewa ne, idan ɗan kudu ne wa ya isa ya kama shi. Mene ba su cewa har akan Buhari, amma me aka yi. Jonathan da matarsa me ye ba ayi musu ba, amma ba mu taba jin irin haka ba. Lokaci ne, saura kwana nawa ne? Ba a dai kyauta ba a sake shi kawai shine kuma a ba shi hakuri.
Ahmed ya ce ” Shugabannin Duniya da matayen su duk ana musu haka, wannan ba sabon abu bane. Amma ni dai tsakani da Allah ta bani kunya matuka.
Discussion about this post