Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya albishirin cewa idan ya hau mulki zai gaggauta yin zaman teburin sulhu da masu tayar da ƙayar bayan jihohin Kudu maso Gabas.
Waɗannan jihohi sun haɗa da Ebonyi, Abiya, Enugu, Anambra, Imo, inda ake fama da tashe-tashen hankulan zubar da jini da kashe-kashe.
Wasu fanɗararrun yankin a ƙarƙashin IPOB sun hana yankin zaman lafiya, a ƙoƙarin su na bijire wa Gwamnatin Tarayya, su na neman sai sun kafa ‘Biafra’.
Yanzu haka shugaban su na tsare ana tafka shari’ar zargin ta’addancin da ake yi masa da kuma tserewa bayan an bayar da belin sa.
A na sa ɓangaren, Tinubu ya ce buƙata ba za ta taɓa biya ta hanyar tashin hankali ba.
Ya ce Najeriya na buƙatar zaman lafiya. Don haka duk wani mai ƙorafi ba za a iya sauraren sa idan ana tashin hankali ba.
Ya ce idan ya ci zaɓen 2023 zai bunƙasa Kudu maso Gabas, kuma zai bunƙasa ilmi domin sai da ilmi ƙasa ke zama ƙasaitacciya.
Tinubu ne ke takara a ƙarƙashin APC, sai dai kuma zai fuskanci ƙarancin ƙuri’u daga Arewa maso Gabas, yankin da a yanzu su ke nuna goyon bayan su da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ɗan yankin su.
Discussion about this post