Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya ba ta da kuɗaɗen da za ta iya ɗauka ta bayar domin daƙile gurɓacewar yanayi da muhalli a Afrika, saboda bashi ya yi wa ƙasar katutu.
Buhari ya bayyana haka ya bakin Ministan Kula da Muhalli, Mohammed Abdullahi, wanda ya wakilce shi kuma ya yi jawabi a madadin sa, wurin taron COP27 da yanzu haka ke gudana, ranar Talata, a Masar.
“Ina sanar da cewa a yanzu Najeriya ba ta da isassun kuɗaɗen da ake buƙata domin zubawa ko tallafawa wajen kula da gurɓacewar. Hakan kuma ya faru ne saboda tulin basussukan da su ka yi wa ƙasashe masu fama da matsin tattalin arziki katutu,” inji shi.
Najeriya a yanzu haka ta na faman gaganiya da bala’o’in ambaliya, wadda ta kawo wa fiye da mutum miliyan 3.2 cikas, kuma ta kashe sama da mutum 600. Sannan kuma ta raba fiye da mutum 100,000 da gidajen su.
Ambaliyar kuma kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, ta lalata fiye da hekta 300 ta gonaki.
PREMIUM TIMES Hausa ta biga maƙalar da Buhari ya aika aka buga a Washington Post, inda ya ce ƙasashen Turawan Yamma munafukai ne.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ƙarara ya kira kasarheni Yamma cewa munafukai ne.
Buhari ya yi wannan kakkausan raddin a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da Taron Magance Illocin Canji Da Gurɓacewar Yanayi (COP27) a Masar.
Shugaban na Najeriya ya yi bayanin a cikin wata maƙala da ya rubuta, kuma aka buga a jaridar Washington Post ta Amurka a ranar Laraba.
Ya kira su munafukai ne saboda a cewar sa, sun kasa cika alƙawarin magancewa da hana ci gaban illolin da canjin yanayi da gurɓacewar yanayi ke haifarwa a Afrika.
Buhari ya tunatar da ƙasashen Turawan Yamma cewa sun yi alƙawarin kashe dala biliyan 100 wajen wannan gagarimin hana illar hayaƙin makamashi yi wa Afrika illa, amma har yau ba su yi komai ba.
“Da yawa daga cikin shugabannin Afrika su na jin haushin yadda ƙasashen Turawan Yamma ke yin biris da wannan gagarimar matsalar da ke addabar Afrika, wadda kuma masana’antun Turai ne ke haddasa ta.”
Ya ce duk wasu bala’o’in da ke faruwa a ƙasashe masu tasowa sanadiyyar sauyin yanayi ko gurɓacewar sa, masana’antun Turai ne ke haddasa su.
“Saboda haka idan ƙasashen Turawan Yamma za su tashi tsaye su tashi su taimaki Afrika, amma su daina shata mana yadda za mu riƙa riƙa amfanin da arzikin mu.” Inji Buhari.
An dai shirya taron COP27 a Masar, saboda ganin cewa Afirka ce matsalar canjin yanayi ta fi shafa a ‘yan shekarun nan.
An haƙƙaƙe cewa yawan fari da ƙarancin ruwan saman da ake samu a wasu ƙasashen Afrika, tsawa da cida mai ruguza gine-gine, fantsamar wutar daji, mummunar ambaliyar ruwa da girgizar ƙasa a Afrika, duk gurɓacewar yanayi ne ke haifar da su, sakamakon illolin gurɓataccen hayaƙin da masana’antun Turai ke jaddadawa.
Discussion about this post