A taron farko na Zauren Tattaunawa Da ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa (Presidential Town Hall), wanda gidan talbijin na Arise TV ta shirya tare da haɗin guiwar kungiyar CDD a ranar 6 Ga Nuwamba, 2023.
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP, Ifeanyi Okowa ne ya fara jawabi a matsayin mataimakin takarar Atiku Abubakar.
Akwai kuma ɗan takarar jam’iyyar LP ta samu wakilcin ɗan takarar ta Peter Obi, sai Rabi’u Kwankwaso ɗan takarar NNPP da kuma Kola Abiola, ɗan takarar jam’iyyar PRP.
PREMIUM TIMES ta shiga Zauren Tattaunawa Da ‘Yan Takara domin ta tantance gaskiya daga shaci-faɗi a cikin jawaban ‘yan takarar.
Yin hakan kuwa zai riƙa magance yaɗa shaci-faɗi yayin da ‘yan Najeriya ke tattauna batutuwan zaɓen 2023.
IƘIRARIN KWANKWASO:
Kwankwaso ya ce lokacin da ya sauka daga mulki a matsayin gwamnan jihar Kano cikin 2015, bai bar bashin ko sisi ba.
TANTANCEWA:
Bayanai daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO) sun nuna cewa lokacin da Kwankwaso ya sake komawa mulki a zangon sa na biyu, a 2011, bashin da ake bin jihar Kano ya kai Dala 59,777,994. Sai kuma waɗansu Naira biliyan 5.8.
Ya bar ofis bayan ya kammala zango na biyu a Mayu, 2016. Binciken DMO ya nuna ana bin Kano Dala 59,796,931. Bashin cikin gida kuma watanni biyar kafin saukar sa, ana bin Kano naira 31,423,625,015. Amma. Lissafi ya nuna bayan Kwankwaso ya sauka da wata shida, bashin cikin gida ya kai naira 65,007,329,454.
Wannan ya na nufin Kwankwaso ya sauka ya bar bashi a jihar Kano tabbas.
IƘIRARIN KWANKWASO 2;
Kwankwaso ya ce yawan sojojin Najeriya ya kai soja 250,000.
Gaskiyar Lamari:
Binciken Global Fire Power na 2022 ya nuna cewa bayan Hukumar Tsaro sun nuna sojojin Najeriya 215,000.
Bankin Duniya shi ma ya ce sojojin Najeriya su 223,000 ne.
Daga baya Kwankwaso ya ce ya na nufin wajen 250,000. Don haka ba lallai ba ne sai sun kai 250,000 ɗin.
Adadin ‘Yan Sandan Najeriya A Bakin Kwankwaso: Ya ce 230,000 ne.
Bincike da shafin yanar gizon Interpol ya nuna su 350,000 ne.
Amma kuma Dataphyte ta nuna su 371,800 ne maza da mata. Wato duk ɗan sanda 1 mutum 540, ƙasa da duk ɗan sanda 1 mutum 450 kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce hakan ke ƙa’ida.
SHACI-FAƊIN PETER OBI:
Peter Obi ya ce Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya shaida masa cewa ‘yan sandan Najeriya su 320,000. “Ku ce ni na faɗi haka,” inji shi.
SHACI-FAƊIN KOLA ABIOLA:
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP, Kola Abiola ya ce Majalisar Ƙolin Tsaron Najeriya ba ta zauna ba tun 1999.
Gaskiyar Lamari: Majalisar Ƙolin Tsaron Najeriya (NSC) zama tun shekaru da dama bayan 1999 har zuwa zaman ta na baya-bayan nan a ranar 14 Ga Oktoba, 2022 ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
SHACI-FAƊIN PETER OBI KAN KYAUTAR GWARZON GWAMNAN KIWON LAFIYA:
Obi ya ce lokacin da ya na gwamna sai da Gidauniyar Bill and Melinda ta ba shi kyautar karramawa ta Gwarzon Gwamnan da ya fi sauran gwamnoni inganta kiwon lafiya a jihar sa.
Gaskiyar Lamari: Bayanan Obi shaci-faɗi ne, kyautar da ya samu ita ce Gwarzon Gwamnan da ya fi sauran gwamnonin Kudu maso Gabas yin hoɓɓasa wajen yaƙi da cutar polio. Bill and Melinda Gates ta bayar da kyautar cikin 2023. Aka haɗa wa jihar sa da tallafin naira miliyan 120.
IƘIRARIN OBI KAN YAWAN ‘YAN SANDAN MASAR:
Obi ya ce ‘yan sandan Masar sun kai miliyan 1. Wannan gaskiya ce. Bincike ya tabbatar da sun haura miliyan 1.
Discussion about this post