Jam’iyyar PDP ta sake fitowa ta bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Bola Tinubu, bai cancanci shugabancin Najeriya ba.
PDP ta fitar da wannan sanarwa a ranar Talata, bayan an watsa wani faifan bidiyo wanda aka nunu Tinubu na cewa, “Allah ya maimaki PDP.”
Tinubu ya yi wannan suɓul-da-baka a Jos, babban birnin Jihar Filato, wurin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sa, a ranar Talata.
Duk da dai bai ƙarasa furta kalmar PDP gaba ɗaya ba, Tinubu ya yi sauri ya koma kan hanya, inda ya ce, “Allah ya taimaki PDAPC.”
Da ya ke maida raddi kan suɓul-da-bakan Tinubu, Sakataren Yaɗa Labaran PDP, Debo Ologunagba, ya ce Allah ne matsi bakin Tinubu ya yi wa PDP kyakkyawar a addu’a, a ranar da Tinubu ɗin ya fara kamfen ɗin sa.
“Tun bayan fitar bidiyon da aka nuno Tinubu ya yi suɓul-da-baka ɗin dai jam’iyyar PDP mazan su da matan su ke cewa ‘amin’.
Debo Ologunagba kuwa cewa ya yi furucin na Tinubu ishara ce daga Ubangiji ya nuna wa APC da sauran ‘yan Najeriya cewa PDP ce za ta iya ceto ƙasar nan daga halin ƙuncin da ta tsinci kan ta a mulkin APC na shekaru bakwai.
“Ko furucin da Tinubu ya yi ya ce Najeriya na cikin mawuyacin hali, ai ya rigaya ya nuna jam’iyyar APC wadda ya ke wa takara da kuma gwamnatin APC su ka jefa jama’a cikin ƙunci.”
Ologunagba ya ce jama’a da dama na ci gaba da yi wa PDP fatan alheri alheri ake ta yi wa jam’iyyar sam-barka, abin da ya ce ƙarara Tinubu ya nuna ba zai iya riƙe mulkin ƙasar nan ba.
A wurin taron kamfen ɗin TInubu a Jos dai an nuno dandazon matasa su na ta antaya antaya jifa a cikin taro.
Duk da magiya da haɗa matasan da Allah su daina yin jifar, sun ɗauki tsawon lokaci kafin su daina.
Sai dai kuma daga baya PREMIUM TIMES Hausa ta ci karo da wani bidiyon da aka nuno wani matashi ya na hayaniyar cewa, “Tunda Buhari ya hau mulki ba abin da ya yi wa Jihar Filato. Duk kuwa da cewa banda Ƙaramar Hukumar Kano Municipal babu kamar Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa wajen tara wa Buhari yawan ƙuri’u a zaɓen 2015 da 2019.”
Matashin ya riƙa kiran matasa da cewa su yi karatun ta-natsu, su daina yin wahalar banza.
Discussion about this post