Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda sama da 50 sannan sun ceto mutum 50 da suka yi garkuwa da su a Arewa maso Yamma da Arewa maso gabas cikin makonni biyu da suka gabata.
Darektan yada labaran hukumar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja da yake bada bayanan nasarorin da dakarun suka samu a aikin samar da tsaro da suke yi a karshen wannan mako.
Danmadami ya ce a Arewa maso Gabas dakarun dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan ta’adda 13, sun kama wasu 10 sannan sun ceto mutum 41 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’adda sama da 13 a harin da sojojin kasa da sama suka kai kauyukan Belowa da Ngwuri Gana, kananan hukumomin Abadan da Bama jihar Borno daga ranar 4 zuwa 5 ga Nuwamba.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa Ali Kwayan da Bukar Mainoka shugabannin kungiyar ISWAP da aka fi sani da sunan kungiyar Shura na kungiyar ISWAP na daga cikin wadanda dakarun suka kashe.
Danmadami ya ce rundunar sojin sama ne ta yi wa motar maharan ruwan bama-bamai bayan ta hango suna dauke da wasu mahara 13 da suka ji rauni daga wani harin da rundunar ta yi wa ‘yan ta’addan.
“A kauyen Ngwuri Gana dake karamar hukumar Bama dakarun sun kashe ‘yan ta’adda da dama a cikin motoci 15
Ya ce akalla ‘yan Boko Haram 250 tare da iyalan su suka mika wuya ga dakarun inda daga cikin su akwai maza 43, mata 80 da yara 121.
Danmadami ya ce dakarun sun kama makamai da kudin su zai Kai Naira miliyan 13.8.
Ya ce dakarun sun ceci mutum 29 da aka yi garkuwa da su inda a cikin su akwai maza biyu, mata 15 da yara 12.
A Arewa maso Yamma Danmadami ya ce a ranar 9 ga Nuwanba dakarun dake aiki a karkashin ‘Operation Hadin Kai’ sun kama wasu mutum biyu da ake zarginsu da safarar bindigogi a Kude dake karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.
Ya ce dakarun sun kama mutanen dauke da harsashi 400 kiran 7.62 mm da Naira miliyan daya a cikin mota.
Danmadami ya ce dakarun sun kama wani dake siyo wa mahara kaya da Naira miliyan 1.5 da jerin kayan da maharan ke bukata a siyo musu.
Ya ce jami’an tsaron sun kama mutumin a shataletalen hanyar zuwa tashar jiragen sama dake Igabi a jihar Kaduna.
Bayan haka Danmadami ya ce jami’an tsaron sun kashe wasu mahara 16, sun kuma kama manyan bindigogi 13 kiran AK-47, harsasai 107 kiran 7.62mm, bam kiran hand grenades 5, babura 75, shanu 150 sannan dakarun sun ceto mutum 19 da aka yi garkuwa da su.
Discussion about this post