Tuni dai jirgin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya cira sama, ba tare da tsayawa roƙon Gwamna Nyesom Wike na Ribas da tawagar sa su shiga a lula tare da su ba.
Hakan da Atiku Abubakar ya yi, ya nuna cewa wataƙila ya na da wani ƙwaƙƙwaran shiri na sarari da na ɓoye, wanda ba dukkan masu lura da al’amurran siyasa ne su ka tsinkayi hakan ba.
Irin yadda aka ga dandazon jama’a a Kaduna da kuma ranar Laraba ɗin nan a Maiduguri wurin gangamin taron PDP, ya nuna cewa jirgin Atiku cike ya ke maƙil da magoya bayan da ko da babu Wike da sauran gwamnoni huɗun da su ke bayan sa, babu yadda za a iya gane cewa akwai wurin da babu fasinjoji a cikin jirgin.
To sai dai kuma lokacin jefa ƙuri’a nan ne ‘yar manuniya ke nunawa. Ko Atiku zai iya yin tasiri a jihohin Ribas, Benuwai, Oyo da sauran jihohi biyun da gwamnonin su ke goyon bayan Wike?
Wannan amsa ta fito daga bakin wani jigo daga manyan dakarun yaƙin 2023 na Atiku Abubakar, wanda ya ce Atiku yanzu haka ya maida hankali kan kamfen, ya rabu da su Wike ‘yan bulkara.
An bayyana cewa tuni ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi watsi da gaganiyar neman sulhu da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da sauran magoya bayan sa.
Wata majiya daga cikin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku ta shaida wa jaridar Vanguard cewa yanzu Atiku ya maida hankali ne kan yaƙin neman zaɓe, kuma hakan ya yi tasiri sosai, idan aka yi la’akari da irin karɓuwar da ya ke ƙara samu a faɗin ƙasar nan.
“Jirgin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na 2023 ya rigaya ya tashi, don haka duk wani tuggu da ƙulle-ƙullen da su Wike za su yi, ba zai haka jirgin kaiwa zango ba.
“Ƙoƙarin da su ka yi da wanda su ke yi domin hana jirgin tashi, bai yi nasara ba. Domin idan ka duba za ka ga a kowane yanki na ƙasar nan Atiku na ci gaba da ƙara samun karɓuwa.
“Wike da sauran gwamnonin da ke goyon bayan sa duk su na da ‘yancin goyon bayan wanda su ka ga dama. Amma fa ba gaskiya ba ce da su ke nuna kan su cewa za su iya hana al’ummar jihohin su zaɓen PDP,” cewar majiyar.
“Maganar cewa su Wike da sauran su na ganin sai wanda su ke so za a zaɓa a jihohin su, wannan duk hauragiya ce kawai. Ka na nufin ka ce Gwamna Seyi Makinde na Oyo na da kwarjinin cewa sai wanda ya ke so za a zaɓa a Oyo? Haba! Shi fa ba Bola Ige ba ne ko Awomolo, to wane kwarjinin hana ‘yan PDP su zaɓi Atiku ya ke da shi?, inji majiyar.
Majiyar ta ce tuni rundunar kamfen ta yi gaba, ba za ta taɓa kowawa kan su Wike ba. “Amma idan mu ka ci karo da su kan hanya, su ka tsayar da jirgin su ka ce a ɗauke su, za mu tsaya su shiga.”
Kwanan nan wasu jiga-jigan PDP da su ka haɗa har da ɗan takarar sanatan Delta ta Tsakiya, Ned Nwoko, sun yi kira ga PDP ta kori Wike, su na cewa ko da shi ko babu shi PDP za ta iya cin zaɓe.
Haka shi ma Gwamna Samuel Ortom na Binuwai, da dama sun ja hankalin sa cewa ya kamata ya yi karatun ta-natsu, ya goyi bayan Atiku Abubakar domin kawo ƙarshen rikice-rikicen makiyaya da manoma a jihar sa.
Discussion about this post