Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi magana a karon farko tun bayan da ya fitar da sabbin launin Naira 200, 500 da kuma 1,000.
CBN dai ya sauya launin kuɗaɗen domin magance tsadar rayuwa, rage kuɗaɗen da ke hannun jama’a, magance buga kuɗaɗen jabu, da kuma daƙile masu karɓar kuɗaɗen fansa.
Sai dai kuma akasarin ‘yan Najeriya sun riƙa sukar CBN, su na cewa sauya kuɗaɗen ba shi da wani tasiri, domin babu wani inganta su da aka yi, sai dai sauya masu launi kawai.
Da dama a kafafen yaɗa labarai da shafukan zumunta an riƙa yi wa sabbin kuɗaɗen shegantaka, ana cewa bula ce aka jiƙa, aka riƙa tsoma tsoffin kuɗin a ciki.
Hakan ya tilasta CBN fitowa a karon farko ya bayyana cewar an buga sabbin kuɗaɗen ne cikin gaggawa, saboda lokaci ya ƙure.
Daraktar Kula da Kuɗaɗe na CBN Ahmed Umar, ya bayyana wa manema labarai cewa ba gaskiya ba ce da ake cewa sabbin kuɗaɗen ba su da inganci, kuma ba su da wata alamar hana masu buga kuɗaɗen jabu kwaikwayon irin su.
Umar ya ce sabbin kuɗaɗen su na da inganci, kuma akwai laƙanin maganin masu buga kuɗaɗen jabu a jikin kuɗaɗen.
Ya ci gaba da cewa buga sabbin kuɗaɗen ya zama tilas, domin a magance matsalolin da su ka taru su ka dabaibaye tasarifin kuɗaɗe a ƙasar nan.
CBN dai ta ce akwai fiye da naira tiriliyan 2 waɗanda ke jula-jula a hannun jama’a, amma ba a kai su banki ana hada-hada da su.
A yanzu kuwa, Umar ya faɗa a taron NDIC cewa ba ma da yawa aka buga kuɗaɗen ba, saboda ana so jama’a su riƙa mu’amala da hanyoyin tasarifin kuɗaɗe na zamani, waɗanda ake hada-hada ba sai an rungumi kuɗi ba. Sai dai a riƙa jin ‘alat’ kawai.
CBN dai ya ce zai fitar da sabbin launin kuɗaɗen a ranar 15 Ga Disamba, yayin da za a daina karɓar tsoffin kuɗaɗe a ranar 31 Ga Janairu, 2022.
Discussion about this post