Hausawa kance, da na gaba a ke gane zurfin ruwa. Kusan za a iya cewa tunda man fetur ya zama wani abu a duniya, ya zamanto arzikin da babu yadda kasashen yamma suka iya da shi, wannan arziki shine ya bawa kasashen masu arzikin sa bunkasa da girma, ko da kuwa wannan kasashe abokan gabar manyan kasashen duniya ne, misali irin su Iran, Russia, Libya da wasu makamantan su.
Nijeriya ta kasance kasa ta 6 ko wani abu makusancin haka a kan arzikin man fetur a duniya, amma har yanzu babu gamsasshan tasiri na wannan arziki walau ga dai-daikun al’ ummar wannan kasa ko kuma kasa baki daya.
Shin zamu iya kwatanta tasirin man fetur din Nijeriay da kasashe irin su Qatar, Saudi Arabia ko Russia? Wasu manazarta a kan siyasar arzikin man fetur a duniya, sun nuna cewa ita Nijeriya arzikin man fetur din ta, wani lokacin ma ya zame mata masifa ne.
A tarihin samuwar man fetur a Kudu-maso-Kudun Nijeriya, ya kafa wani irin tarihi, na farko dai har yau baza a iya cewa wannan arzikin ya fidda su daga cikin talauchi ba, kai hatta sana’oin su na gado, na kamun kifi da noma ma, wanna arziki ya tagayyara su, saboda gurbacewar yanayin su.
Tasirin man fetur din Nijeriya a kan tsaro kuwa, shima wani mummunan batu ne, domin kuwa mutane da dama sun rasa rayukan su, har da manyan mutane da sarakuna, sabo da rigima a kan kokuwar neman arzikin Man Fetur. Dubban mutane suna mutuwa, saboda fasa bututun man fetur.
Kai har a wannan lokacin, batun bai canja ba, kawai shahararrun tubabbun yan ta’adda ne suke cin moriyar wannan arzikin, saboda manyan kwangilar bututun da a da su suke fasawa, kuma yanzu a ka tsaron su. A yau za a iya cewa, duk jahohi masu arzikin man fetur, babu wasu aiyuka manya da za iya fada don taimakon al’umar su, ita kan gwamnatin tarayya kullum a cikin cin bashi take, kuma al’umar wannan kasar kullum suna rugawa cikin matsanan cin talauchi.
Samun Man Fetur a Arewacin Nijeriya, kusan shekaru talatin da suka wuce a ka soma tunanin tabbatarwa da hako wannan Man Fetur wato Kolami Oil wanda yake a tsakanin jahar Gombe da Bauchi, za a iya cewa duk kokarin gwamnatocin baya da kuma tasirin siyasar Nijeriya ta Kudu da Arewa, wannan aikin yayi ta samun tasgaro. Gwamnati mai ci ta Muhammadu Buhari, za a iya cewa tayi rawar gani wajen tabbbatar da wannan aiki, a shekara 2019, 2 ga watan February ne Shugaba Buahri ya kaddamar da fara tona rijiyar man a wannan wuri.
Yanzu za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, saboda an gano samun Gangar Man Fetur har Litta Miliyan Dubu Daya (60 Billion Barrel of Crude Oil), Bilayan 500 na Gas (500 Billion of Cubit Feet of Gas).
A ranar watan November 2022, ranar 22 ga watan, Shugaba Buhari ya kafa sabon tarihi wajen kaddamar da hako wannan Man Fetur, wanda zai samar da Matatar Man Fetur, wanda zata tace kimanin Gangar Man Fetur 120,000 a ko wace rana. Sannan kuma za a samar da kamfanin sarrafa Gas har Miliya 500 a rana. Sannan za a samar da Wutar Lantarki kimanin Megawatt 300, da kuma samar da kamfanin Takin Zamani, wanda zai samar da ton 2,500 a ko wace rana. Tabbas wannan abin alfahari ne ga Nijeriya, musamman mutanen arewacin Nijeriya domin tabbas in har hakan ta tabbata, ba kawai jahohin Bauchi da Gombe ba harma sauran jahohin Arewa arzikin su zai bunkasa.
Amma abin tambaya a nan shine, Shin wannan arziki ba zai iya zama bala’I ga mutanen arewacin kasar ba?
Zamu iya misalta wannan Man Fetur da irin na kasar Nijer, domin baya kusa da Teku kamar irin yadda na kudancin Nijeriya yake, wanda a kwai wahala sosai in har ana so a kais hi bakin Teku don sayarwa a kasuwannin duniya, zai fi alfanu in aka sarrafi a nan kamar yadda Nijeriya ke son yi. Amma mu sani ko su a kasar Nijer din, al’umomin da a ka sami wannan Fetur din a wajen su, kuka sukeyi, maimakon su ci gaba baya suke yi.
Sai gashi kuma, har wa yau, wannan arziki ya zo a lokacin da Arewacin Nijeriya ta ke cikin wani yanayi marar kyawu. Yan Arewa su da Shugabannin su, sun yi gangancin maida yankin sansanin ‘Yan Ta’adda, hatta sana’ar noma ya gagare su, kullum kashe su a keyi da kuma sace su don karbar kudin fansa, a wasu wuraren fa tamkar babu gwamnati, sai manoma sun biya diyyar miliyoyin kudade, kafin a barsu suyi noma. Wanna fa noma fa kenan da kiwo.
Man Fetur din Arewa kan iya zama bala’I a kan su? In har ba ayi karatun ta nutsu ba, wannan arziki kan iya zama bala’I, kuma moriyar sa ta zama kadan, kamar yadda ya ke a kudan cin Nijeriya wanda kawai wasu kalilan ne suke wadaka da irin wannan arzikin, su kuma sauran mutanen suna cikin bala’in, gonakin su da kogunan su, sun gurbace, kamun kifi da noma ya gagare su, suna mutuwa a hannun militant.
In har ba a yi dogon nazari a abin da zai biyo baya, to tabbas za a gwammaci kida da karatu.
Kawai za iya samu nasara ne, in har shugabanni sun chanja tunanin su, sun mai hankali wajen adalci da kin rashawa da sata, da kuma tunanin al’umar su a kan komai.
alhajilallah@gmail.com