Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin ganin dan takarar shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu ya kai ga nasara a zaben dake tafe.
Buhari ya bayyana haka a wajen taron Kamfen din jam’iyyar APC da aka yi a garin Jos, Jihar Filato.
A cewar sa, shugaba Buhari ya bayyana wa miliyoyin magoya bayan jam’iyyar APC cewa bai zo garin Jos don ya karanta doguwar jawabi bane, ” Na zo ne domin in mika tutar APC ga dantakarar shugaban kasan mu, wanda zai gaje ni, wato Bola Tinubu.
” Jam’iyyar mu ta dauki matsaya kuma matsayar ita ce, Tinubu, saboda haka dukkan mu za mu dunkule mu yi aiki tukuru don ganin Tinubu da jam’iyyar APC sun kai ga nasara. Wannan tafiya ta mu ce duka kuma babu gudu ba ja da bawa, nasara ce kawai a gaban mu kuma ita muke bida.
A jawabin sa, shugaban APC ta kasa, Sanata Adamu Abdullahi ya shaida cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zarce alkawuran da ya dauka a lokacin da yaki neman takarar shugaban cin Najeria.
” Duka alkawuran da Buhari ya dauka ya cika su cif-cif har ya zar ce yadda ake tsammani.
Discussion about this post