Kamar yadda jami’in rundunar ƴan sandan jihar Barno Zagazola Makama, ya bayyana cewa wani mutum mai sana’ar saida kifi ya kawo karar wata akuya cewa ta cinye masa tarin kifi da ya kasa don siyarwa.
A karar da ya shigar ya ce wannan akuya ta fi shekara biyar tana yi masa ta’adi kuma ya sanar wa mai akuyar.
Ibrahim wanda akuyar ta yi masa ta’adi ya ce ” A wannan rana,, akuyar ta rika lallaɓowa ta fako na, nima kuma na ki matsawa. Amma kuma sai ta yi kamar ta tafi, ashe ta laɓe ne, da ga tashi da na yi ƴan mintoci sai ko ta diran ma kifin nan ta lamushe su tas.
Ibrahim ya kara da cewa ta daɗe ta na yi masa ta’adi amma wannan da ta yi ya fi baƙanta masa rai domin ya yi asara mai yawan gaske ne.
Sai dai kuma Lubabatu Mohammed wacce akuyar ta ce, ta roki da a yi mata sassauci a saki akuyar, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta buga.
” Idan aka saki akuyar zan saida ita, ko in yanka ta mu cinye ko kuma in rika ɗaure ta wuri daya.
Discussion about this post