Jami’an Hukumar EFCC sun dira cibiyar ƴan canjin Abuja, dake Zone 4, inda suka kama masu canji da dama.
Wakilin PREMIUM TIMES da ya ke wurin a lokacin da abin ya faru ya ce jami’an sun zo wannan wuri ne cike a mota kirar Bus sannan suka fara cafke mutane masu hadahadar canjin dala.
Wani ɗan kasuwa da ke sana’ar canjin daya ya shaida wa wakilin mu cewa yanzu haka ma babu dalar a kasuwar canjin, amma kuma da misalin karfe 1-2 na rana, dala 1 tal ta kai naira 900.
Dala ta zama gwal a Najeriya yanzu tun bayan ayyana sauya fasalin naira da babban bankin Najeriya ya yi a cikin makin jiya.
Rugujewar darajar Naira
Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke iƙirarin cewa ya cika wa talakawan Najeriya burin su na dalilin zaɓen sa a 2015, a daidai lokacin ne kuma darajar Naira ke ci gaba da lalacewar da ba ta taɓa yi ba a tarihi.
A ranar 31 Ga Oktoba, an sayar da sayar da dala Naira 803, a ranar Juma’a kuma an sayar Naira 781.
An danganta tsadar dala da sanarwar da Gwamnan Baban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi cewa za a sabunta launin Naira 200, 500 da 1,000.
A tarihin Najeriya dai naira ba ta taɓa yin irin wannan tashin-gwauron-zabo ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki cikin 2015 cike da alƙawarin daidaita darajar Naira da Dalar Amirka, wadda a lokacin da ya hau mulki ana kukan ta kai naira 200.
Shekaru bakwai da rabi bayan hawan Buhari, maimakon Naira ta ƙara daraja, yau sai ga shi ta yi rugujewar da ta kai dala ɗaya daidai da Naira 803.
Yayin da aka riƙa kuka da matsalar faɗuwar darajar Naira zamanin Jonathan, yanzu kuma da ta nunka lalacewa har sau huɗu, an ta cewa har ma gara lokacin Jonathan sau dubu.
Ana wannan fama ne a lokacin tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa da tsadar abinci a faɗin ƙasar nan.
Hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram ya gurgunta miliyoyin jama’a ta yadda duk wata matsalar da ta bijiro cikin ƙasa, ba ta gushewa, sai dai ta samu wurin yin zaman dirshan.
Masu harkar canjin da PREMIUM TIMES ta zanta da su a Abuja da Uyo, sun danganta tsadar dala da azarɓaɓin sauya launin kuɗin da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi.
Discussion about this post