Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya gana da shugabannin Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), a ranar Laraba.
Wata sanarwa da Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Okowa ta fitar, ta bayyana cewa an yi ganawar a Sakateriyar CAN ta ƙasa da ke Abuja.
Cikin tawagar Tinubu akwai matar sa Oluremi Tinubu, wadda ita ma Kirista ce, mataimakin takarar Tinubu, Kashim Shettima, Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Gwamnonin Imo Hope Uzodinma, Kano Abdullahi Ganduje, Ebonyi David Umahi da na Kwara Abdulrahman Abdulrasaq.
Sauran sun haɗa da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Ajayi Borroffice, Bulalar Majalisar Dattawa, Orji Kalu da Ministan Ayyukan Musamman, George Akume.
Shugaban CAN Daniel Ukoh ya gabatar wa Tinubu buƙatu da dama, waɗanda a cikin su akwai kamar haka:
“Sun buƙaci a bar kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta, a rage ƙarfin ikon gwamnatin tarayya a bai wa jihohi, a bai wa mabiya addinai haƙƙin dama daidai da kowane addini. A bai wa kowace ƙabila ‘yancin dokar haƙƙin zamantakewar su. A bai wa al’ummar da ke da arzikin albarkatun ƙasa ikon damƙa masu wuƙa da naman arzikin yankin su, a haramta kiwon shanu sakaka, kuma a bai wa kowa ‘yancin zaɓe ko tsayawa takara, tare da gina tsarin zaɓe mai nagartar ba kowa damar tsayawa takara ko yin zaɓe.”
Tinubu ya shaida masu cewa zaɓen wanda zai yi masa takarar mataimakin shugaba abu ne da ya kasance masa mai wahala.
Amma ya ce ya ɗauki Kashim Shettima saboda cancantar sa, tare da tabbacin cewa shi ne zai iya taya shi cimma ƙudirin sa na bunƙasa Najeriya.
Discussion about this post