Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai tare da sauran gwamnoni uku masu adawa da takarar shugaban ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, sun kai wa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ziyara a ranar Laraba.
Ortom ya samu rakiyar Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Daga cikin hasalallun gwamnonin biyar, Gwamna Seyi Makinde na Oyo ne bai samu damar kai wa Gwamna Bala ziyarar ba.
Ortom wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP Masu Muradin Gaskiya, ‘yan G5, sun yi ganawar sirri da Bala a cikin Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.
Wike ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, inda ya fara da bayar da haƙurin rashin zuwan Gwamna Makinde na Oyo, saboda ba ya ƙasar.
Ya ce sun je ne domin su jajanta masa kuma su goya masa baya a kan saɓanin sa da Atiku Abubakar.
“Mun zo Bauchi domin mu ji abin da ya faru da shi, kuma idan akwai hanyoyin da za mu iya ba shi shawarwari nagari.
“Duk abin da ya shafi Gwamna Bala, to mu ma ya shafe mu. Dalilin zuwan mu kenan ba wani abu ba,” inji shi.
Da ya ke magana, Gwamna Bala ya ce ya yi farin cikin karɓar baƙuncin gwamnonin waɗanda su ka je domin nuna masa goyon baya. Ya ƙara da cewa Bauchi a gidan su ne.
“Su na kiran kan su PDP G5, ai ya kamata a ce ina cikin su, amma sai su ka maida ni saniyar-ware saboda wani dalili na su.
“Amma duk da haka babu ranar da ba zan yi waya da ɗaya daga cikin su ba. Saboda ai wanda ra’ayin ku ya zo ɗaya ai shi ne abin tuntuɓar ka kuma abin shawarar ka a kullum.
“Abin da ya fi burge ni game da su shi ne su na da ƙarfin jure dafin kibiyar duk wani ƙalubale.
“Ra’ayi na ya ɗan sha bamban da na su, amma dai ina jin zafin abin da aka yi masu, su ma su na jin ciwon abin da aka yi min.
“Mu na fuskantar ƙalubale a Bauchi, musamman na masu yin ‘anti-party’, masu shirya tuggu da ‘yan kitsa sharri,” inji Bala.
Bala ya ce ziyarar da gwamnonin su ka yi masa ta ba shi damar sanar da su damuwar sa, fargabar sa da kuma gagarimin hadarin ya zai iya tirniƙe su nan gaba.
Bala dai ya na cikin Rundunar Yaƙin Atiku Abubakar. Shi ne Mataimakin Kwamandan Arewa. Haka shi ma Seyi Makinde na Oyo, shi ne Mataimakin Kwamandan Kudu.
Bala na cikin ‘yan takara, amma ya samu ƙuri’u 20 kacal.
Discussion about this post