Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom, wanda kuma shi ne Shugaban Kamfen ɗin PDP da Atiku Abubakar na zaɓen 2023, ya bayyana cewa tabbas jam’iyyar su ta tafka kuskuren da ya janyo mata matsala a yanzu.
Sai dai kuma ya ce hakan ba zai kashe jam’iyyar ko ya nakasa ba, maimakon haka, cewa ya yi ba da daɗewa ba za a ɗinke ɓarakar.
“Ai tsakanin kwano da cokali ma a kan kabre da faɗa, amma kuma su sake haɗuwa a wuri ɗaya.”
Da ya ke magana a kan hasalallun gwamnoni biyar waɗanda su ka bijire wa takarar Atiku Abubakar, Gwamna Emmanual ya ce har yanzu gwamnonin su na cikin PDP.
“Dukkan su biyar su na cikin PDP, ba su fita ba. Shi ya sa na ce za a sasanta ba da daɗewa ba.
“Kuma abin da za ku lura shi ne, dukkan waɗannan gwamnoni biyar, ɗaya ne kaɗai ba zai sake yin takara a ƙarƙashin PDP ba. Sauran huɗun za su yi takarar gwamna karo na biyu a PDP. Kenan ba za su bari jam’iyyar ta faɗi zaɓe ba.” Inji Emmanual.
Da ya koma kan cancantar Atiku Abubakar kuwa, Gwamna Emmanual ya ce Atiku ne ya fi sauran ‘yan takara cancanta.
Emmanual ya yi wannan tattaunawar ce da jaridar THISDAY, sati ɗaya bayan hasalallun gwamnonin PDP biyar sun ce ɗan Kudu za su zaɓa a 2023.
Discussion about this post