Hasalallun Gwamnoni 5 masu neman sai an cire Shugaban PDP Iyorchia Ayu, sun kafa ƙungiyar da su ka kira ‘Integrity Group’, kuma G5.
Gwamnonin sun haɗa da Nyesom Wike na Ribas, Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benuwai, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu na Abiya. Sun kafa ƙungiyar ta Nagartattun PDP 5 a Legas, a ranar Lahadi.
Gwamnonin biyar sun je taron sanye da ankon fararen rigunan da su ka barranta da sauran ‘yan PDP.
Gwamnonin dai sun tuma tsalle sun ƙi amincewa da takarar Atiku Abubakar, bisa sharaɗin tilas sai Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu shugabancin PDP tukunna.
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya shaida wa manema labarai cewa sun kafa G5 ɗin ne domin ci gaba da aikin da su ke yi na kare martabar PDP da kuma tabbatar da an yi adalci a rabe-raben mukamai cikin jam’iyyar.
Ba a dai san dalilin da ya sa su ka je har Legas su ka yi taron a can ba, jihar da APC ce me mulkin ta, kuma can ne ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya ke.
Idan za a tuna dai har yau waɗannan hasalallun gwamnonin ba su shiga rundunar yaƙin neman zaɓen Atiku/Yakowa ba, kwanaki 48 bayan fara yaƙin neman zaɓe da jam’iyyu su ka fara.
Discussion about this post