Yanzu dai ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya amince da tayin neman yin sulhu da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da magoya bayan sa su ka nema.
Wike da wasu gwamnoni huɗu sun janye daga shiga ko goyon bayan takarar shugabancin ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, har sai an biya masu buƙatar cire Shugaban PDP Iyorchia Ayu, an maye gurbin sa da ɗan Yankin Kudu tukunna.
Sun nuna rashin amincewa da fitowar ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iyya daga ɓangare ɗaya, wato Arewa.
Atiku ya kuma nuna cewa ya amince da sasantawa da su Wike ɗin domin a kawo ƙarshen rikici da dambarwar da su ka dabaibaye PDP.
Ya ce yin hakan abu ne mai muhimmancin da zai ƙara haɗa kan ‘yan jam’iyya, sannan ya ƙara ƙarfafa PDP ƙwarai da gaske.
Atiku ya yi tsinkayen cewa tun da aka fara wannan dambarwa da Wike da ‘yan ɓangaren sa, bai taɓa rufe masu ƙofar shiga a sasanta ba.
Daga nan ya yi kira ga dukkan shugabannin jam’iyya da magoya bayan ta su kasance masu goyon bayan wannan ƙoƙarin sasanci.
Idan ba a manta ba, bayan ɓangaren Wike ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, sun shaida wa manema labarai cewa har yanzu ƙofar zama a sasanta tsakanin su da Atiku da PDP a buɗe ta.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Atiku mai suna Paul Ibe ya fitar, ya ce sasancin shi ne mafi alheri domin a ƙara wa jam’iyya ƙarfi, karsashi, sannan kuma a samu haɗin kai baki ɗaya.
Sannan kuma a wurin ne Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi afuwar zafafa kalaman da ya yi kan Atiku, inda ya ce da ya zaɓi Bafulatani, gara ya mutu.
Discussion about this post