Gwamnatin Najeriya ta ce ta na nan kan bakan ta na matsayar da ta ɗauka dangane da yajin aikin malaman jami’o’i, inda ta ce ‘idan ba ka yi aiki ba, to ba ka da albashi.
Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka, abin da ke nufin cewa ba za a biya malaman jami’o’i albashin su na watanni takwas da su ka yi su na yajin aiki ba.
Adamu ya jaddada wannan matsaya ta Gwamnatin Tarayya, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, a ranar Laraba.
Minista Adamu ya ƙara jaddada wannan bayani ne lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya ce ba za a biya albashi ga duk makamin da bai yi aikin koyarwa ba.
Sai dai kuma ya ƙaryata rahotannin da ke cewa gwamnatin ta maida malaman jami’o’i ma’aikata na wucin-gadi, maimakon na dindindin ɗin da su ke kafin a yanke masu albashin watan jiya.
Gwamnatin Najeriya ta yanke wa malaman jami’o’i albashin watan da su ka karɓa bayan komawa aiki daga yajin aikin watanni takwas.
Ita dai gwamnati ta ce ba za ta biya malaman jami’o’i albashin watan Fabrairu zuwa Octoba ba, saboda a tsawon watannin takwas duk yajin aiki su ke yi.
Baya ga ASUU, gwamnati ta riƙe albashin sauran ƙungiyoyin ma’aikatan gwamnatin tarayya da su ka tafi yajin aiki har na tsawon watanni huɗu.
Kungiyoyin da abin ya ritsa da su sun haɗa da SSANU, NAAT da NASU.
A watan Oktoba dai gwamnati ta biya malaman jami’o’i albashin kwanaki 18 kaɗai, waɗanda ta ce su ne malaman su ka shafe bayan komawa yajin aiki kafin watan ya ƙare.
Tuni dai wannan mataki da gwamnatin tarayya ta ɗauka ya sake jefa ASUU shiga zanga-zangar ƙin amincewa da matakin.
Da farko Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani, inda ya ce ya na da ran za a biya malaman albashin na su na watanni takwas, amma tsitstsinka masu za a yi.
Sai dai kuma kalaman da su ka fito daga bakin Ministan Ilmi a ranar Laraba, sun nuna cewa gwamnati ba za ta biya su albashin na watanni takwas ɗin ba.
Discussion about this post