Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Alhassan Doguwa, ya ce ‘yan ta-kifen siyasa ne su ka kai wa tawagar sa mummunan hari a filin jirgin Malam Aminu Kano a Kano, har su ka ragargaza motar sa.
Doguwa ya ce yayin da aka yi masa kwanton-ɓauna a daidai ƙofar shiga filin jirgin, maharan sun raunata magoya bayan sa da dama, sannan kuma sun sace motar sa a unguwar Gandun Albasa, kusa da gidan Bashir Tofa a wani farmakin da aka kai wa tawagar ta sa, daban da na filin jirgin sama.
Rikici dai ya ɓarke a cikin APC a jihar Kano, tun a ranar Litinin ta makon shekaranjiya, bayan da aka ce Doguwa ya kai wa ɗan takarar mataimakin gwamna, Murtala Garo hari a wurin wani taro a gidan Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna, wanda shi ne ɗan takarar gwamna na APC a Kano.
An ce Doguwa ya ranƙwala wa Garo jifa da kofin shayi a wurin taron.
Doguwa ya ce ya yi mamakin farmakin da aka kai masa, saboda ya rigaya an yi masa sulhu da Garo, sun sasanta, bayan Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya shiga tsakanin su. Ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ma ya shiga tsakani, ya sasanta su.
“An lalata min fastocin kamfen da manyan ƙyallayen tallata ɗan takara a daidai ƙofar shiga filin jirgin sama na Kano, kuma an lalata min mota. To na san waɗanda su ka turo ‘yan ta-kife aka yi min ɓarna,” inji Doguwa.
Yayin da ya ce magoya bayan sa su kwantar da hankali kada su yi ramuwar-gayya, ya ce an raunata magoya bayan sa da adduna, inda ya ƙara da cewa yanzu haka uku daga cikin su na kwance asibiti su na jiyya. Akwai kuma wasu uku da aka sallama bayan an kwantar da su a asibiti.
“Motar da ke ɗauke da ‘yan Mazaɓa ta an kai mata hari daidai kusa da gidan Bashir Tofa, ‘yan iska sun sassari da dama daga cikin su. Wasu har yanzu su uku na asibiti kwance, wasu ukun kuma an sallame su. Sannan an sace min mota. Amma na san waɗanda su ka turo a yi min haka,” cewar Doguwa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Kiyawa ya ce har lokacin tattara wannan labari ba a kai masu rahoton hargitsin ba.
Discussion about this post