Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta umarci INEC ta ƙwace takarar da Hamza Al-Mustapha ke yi ta shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar AA.
Da ake yanke hukuncin a ranar Juma’a, kotu ta umarci INEC kuma ta soke dukkan ‘yan takarar AA a matakan zaɓen gwamnoni, ‘yan majalisar wakilai ta ƙasa, sanatoci da ‘yan takarar majalisar dokoki baki ɗaya.
Soke takarar su da kotu ta yi ya zo ne dalilin hukuncin da kotun ta yanke cewa shugaban jam’iyyar AA wanda ya bayar da sunayen su bayan kammala zaɓen fidda gwani, ba shi ne halastaccen shugaban AA ba.
Shugaban ɗaya ɓangaren masu jayayya na AA, Kenneth Udeze ne ya miƙa wa INEC sunayen su Hamza Al-Mustapha, bayan kammala zaɓen fidda-gwani a cikin Juni, a Abuja.
Kotu ta ce Udeze ba halastaccen shugaba ba ne, don haka dukkan ‘yan takarar da aka zaɓa a ƙarƙashin shugabancin Udeze, sun tashi a tutar babu.
Saboda haka nan take kotu ta ce INEC ta karɓi dukkan sunayen ‘yan takarar da su ka ci zaɓen fidda-gwani na ɓangaren ɗaya shugaban jam’iyyar, wato Adekunle Omoaje.
Hamza Al-Mustapha dai shi ne Babban Dogarin tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha.
Rikicin da ya dabaibaye AA ya taso ne tun bayan kammala zaɓen 2019.
Amma wannan sabon dai shi Adekunle ne ya garzaya kotu a cikin watan Disamba, inda ya roƙi kotun cewa ta ruguje dukkan zaɓukan fidda gwani da AA ta yi a ɓangaren Kenneth Udeze.
Discussion about this post