Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas ba za su tafka irin kura-kuran d yankin Neja Delta masu arzikin man fetur su ka tafka ba.
Yahaya ya bayyana haka a ranar Talata, a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels.
A ranar ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da fara aikin haƙo ɗanyen mai a Kolmani, yankin Bauchi da Gombe.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin fara haƙo ɗanyen mai a Kolmani, yankin da ke jihohin Bauchi da Gombe.
Wannan wani tarihi ne mai tabbatar da samun ɗanyen mai a Arewa, bayan shafe shekaru ana ta fafutikar aikin nema.
Cikin watan Oktoba, 2019 ne NNPL ta tabbatar da cewa an gano akwai ɗanyen mai da gas a ƙarƙashin ƙasar yankin Kolmani, kuma mai tarin yawan gaske.
Wurin wanda ke da faɗin gaske, ya shafi yankin Upper Benue Basin har zuwa Gongola Basin.
Kamfanin Sterling Global Oil, NNDC da NNPCL ne za su yi aikin haƙo ɗanyen man a Yankin Kolmani Oil and Gas Field.
Da ya ke ƙaddamar da fara haƙar ɗanyen man a Bauchi, Buhari ya ce aƙalla akwai ɗanyen mai a yankin fiye da ganga biliyan 1, kuma akwai gas zai kai cubic biliyan 500.
An dai daɗe ana gaganiyar neman ɗanyen man har zuwa cikin Oktoba, 2019 lokacin da aka tabbatar da samun sa.
Buhari ya ce samun ɗanyen man zai bunƙasa tattalin arziki, samar da aiki, samar da kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar mutanen yankin.
Ya ce ya zauna da Gwamnonin Gombe da Bauchi ya umarce su da su sa ido sosai, saboda aikin haƙar ɗanyen mai ɗin ya shafi mazauna yankin.
An samu arzikin ɗanyen man fetur a yankin Neja Delta tun cikin 1956.
Gwamna Yahaya:
Da ya ke magana kan yadda za a riƙa kula da arzikin ɗanyen man, Yahaya ya ce ma’aikatun kare muhalli na jihohin za su haɗa hannu da ma’aikatar muhalli ta tarayya domin kare rayuka da lafiyar mazauna yankin da za a fara haƙo ɗanyen man.
Ya ce gwamnati za ta yi dukkan ƙoƙarin da za ta yi domin ta kauce wa afkawa cikin irin ramun da yankin Neja Delta ya riƙa afkawa a batutuwa da aikace-aikacen da su ka shafi haƙo ɗanyen mai a yankin Neja Delta.
“Mun rigaya mun koyi darussa. A irin abin da ya riƙa faruwa a Neja Delta da sauran wuraren da ake haƙo ɗanyen mai, babu gwamnatin da za ta bari a ci gaba da samun irin waɗannan matsaloli.
Ya ce akwai jami’an tuntuɓa da ke ilmantar da Jihar Gombe dangane da abubuwan da su ka dace ta yi musamman batun samar da ƙwararrun da za su yi aiki a wurin, ma’aikata da masu aikin ƙarfi da sauran su, domin a samu gagarimar nasarar cimma riƙa haƙo ɗanyen mai ɗin.
Discussion about this post