A yayin da za a yanke wa ɗan damfara Hushpuppi hukuncin laifin aikata zambar da ake tuhumar sa a Amurka a ranar Litinin ɗin nan, matar sa da wasu limamai sun rubuta wa Kotun Gundumar Tsakiyar California a Amurka cewa tunda ya yi nadama, kuma ya ce zai biya waɗanda ya damfara, to a sassauta masa hukunci, kada a ɗaure shi tsawon shekaru masu yawa.
Limaman da su ka aika da wasiƙun a ranar 4 Ga Nuwamba, 2022, sun haɗa Limanin Masallacin Imisi Oluwa, Rasaq Olupede da kuma Liman Malam Hudu Abdul’aziz, na Masallacin Madarasatul Ahlul Bait da ke Maiduguri.
Yayin da Liman Razaq ya bayyana cewa Hushpuppi mutumin kirki ne da ke taimaka wa masallacin da tallafi, shi kuwa Liman Abdul’aziz cewa ya yi a cikin wasiƙar, Hushpuppi mutum ne mai taimakon marayu, matan da mazan su su ka mutu su ka bar su cikin rayuwar ƙunci da sauran mabuƙata.
Su biyun sun nuna cewa tuni Hushpuppi ya tuba, ya Yi nadamar laifin da ya aikata, kuma ya yi alƙawarin ya daina harkar damfara.
Ita ma matar sa mai suna Regina Manneh, ta ce yanzu mijin na ta ya tuba, kuma ya yi alƙawarin idan ya fito ba zai sake damfara ba.
Idan ba a manta ba, watannin baya Hushpuppi ya rubuta wa Mai Shari’a Otis Wright wasiƙa daga kurkuku, inda ya ke neman afuwa ko sassaucin yawan shekarun zaman gidan kurkuku, tare da tuba, nadama da alƙawarin zai biya waɗanda ya damfara ɗin kuɗaɗen su.
Mai gabatar da ƙara dai na so aƙalla kotu ta yanke wa Hushpuppi mai shekaru 40 a duniya, hukuncin ɗaurin shekaru 11 a kurkuku.
Discussion about this post