Akwai ƙasashe da dama su ke da ‘yan wasan da ba a cikin ƙasar su aka haife su ba. Yawancin ‘yan wasan iyayen su su je wata ƙasa ne da zama, aka haife su a can.
Ga wasu ƙasashe biyar da su ka fi yawan ‘yan wasan da ba a cikin ƙasar da su ke buga wa wasa aka haife su ba.
1. MOROCCO: ‘Yan Wasa 14:
‘Yan wasa 14 da cikin 26 da Morocco ta tafi da su, duk a ƙasashen waje aka haife su, ba a cikin Morocco ba.
Daga cikin irin su akwai Ashraf Hakimi na PSG wanda aka haifa a Spain da kuma Hakim Ziyad da aka haifa a Netherland.
2. TUNISIYA: ‘Yan Wasa 12:
‘Yan wasa 12 na Tunisiya duk a ƙasashen waje aka haife su. Guda 10 a cikin 12 ɗin kuwa duk a Faransa aka haife su.
3. SENEGAL: ‘Yan Wasa 12:
4. QATAR: ‘Yan Wasa 11:
Qatar ta kafa dokar neman fitattun ‘yan ƙwallon da ke son zama ‘yan ƙasar, tun bayan da ta fara shirye-shiryen ɗaukar nauyin Gasar Kofin Duniya.
Daga ciki ƙungiyar ƙwallon ƙafar Qatar, 11 ba a ƙasar aka haife su ba.
5. WALES: ‘Yan Wasa 10:
‘Yan wasa 10 na ƙasar Wales duk ba haifaffun cikin ƙasar ba ne. Guda 9 a cikin su a Ingila aka haife su, shi kuma ɗayan a Spain.
Discussion about this post