Kotun Ɗaukaka Ƙara ta saɓule wa ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya wandon takara, ta ɗaura wa Laila Buhari.
A ranar Laraba ce kotun ta yanke hukuncin cewa zaɓen da aka yi wa Nuhu Abubakar ba a ƙarƙashin halastattun shugabannin jam’iyya aka zaɓe shi ba.
Yayin da aka zaɓe Laila Buhari a ƙarƙashin shugabancin Shehu Sagagi, shi kuwa Nuhu Abubakar an zaɓe shi ne a ƙarƙashin wani ɓangaren shugabannin daban, waɗanda kotun ta ƙi amincewa da shugabancin su.
Sagagi dai mai goyon bayan Rabi’u Kwankwaso ne, kafin Kwankwaso ɗin ya fice daga PDP ya koma NNPP.
Ranar 26 Ga Satumba ce Babbar Kotun Tarayya ta kori ƙarar da aka maka Sagagi.
Sai dai kuma a ranar Laraba Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukuncin ƙwace takarar Nuhu, ta damƙa wa Laila Buhari.
Jam’iyyar PDP na fama da turnuƙun rikici daga sama har ƙasa. Baya gafandarewar da hasalallun gwamnonin nan biyar a ƙarƙashin Nyesom Wike na Jihar Ribas su ka yi, a Kano ma jam’iyyar na fama da rashin takamaimen ɗan takarar gwamna. Sannan kuma ta rasa karsashin ta tun bayan ficewar Kwankwaso da Peter Obi daga jam’iyyar.
Discussion about this post