Ɗan takarar shugaban kasa na APC kuma tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya maida wa gwamnan jihar Peter Soludo martani game da yarfar da yayi masa cewa karambani ne kawai ya sa ya fito takarar shugaban kasa.
Obi ya ce” Ay kai babban wa na ne, ka ma fini ilimi tunda har ka kai matsayin farfesa, sai ka nuna bajintar ka yanzu tunda kaine gwamna, ka yi abin da suka zarce nawa. Ba a baki abin yake ba ko a takardar farfesan ci.
Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra, ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ba zai yi nasara a zaɓen 2023 ba.
Obi da ke jam’iyyar APGA, wadda Obi ya fice ya koma PDP, kafin ya koma LP ya tsaya takara, ya ce, “shi ma Obi ɗin ya san cewa ba zai yi nasara ba. Kawai dai burga ce da kuma ci-da-zuci, sai kuma rashin mutuncin da magoya bayan sa ke yi wa mutanen da ba su goyon bayan LP.”
“Mu faɗa wa kan mu gaskiya. Peter Obi dai ya san ba zai iya yin cin zaɓen shugaban ƙasa ba. Kuma ba cin zai yi ba ma. Shi dai ya san salon wasan da ya ke takawa, kuma mu ma mun san irin salon wasan da ya ke takawa. Shi ɗin ma ya san mun san dalilin da ya ke taka irin wannan salon wasan ƙwallo da ya ke yi. Ai irin salon wasan da ya ke yi ne ya sa ya ƙi komawa APGA,” inji Soludo.
“Gaskiyar magana jam”iyyu biyu ne ko kuma ‘yan takara biyu ne kaɗai masu karsashin iya cin zaɓe, kuma su ke yin da gaske a zaɓen shugaban ƙasa. Sauran ‘yan dirama ne kawai!” Haka Obi ya bayyana, amma bai ambaci sunayen kowa ba.
“Duk da ina yi wa LP fatan alheri ita da Peter Obi ɗan takarar ta, amma na shaida masa cewa ba zai iya cin zaɓe ba. Ni a zuciya ta haka na ke da dabbacin cewa ba cin zaɓe zai yi ba. Kuma a cikin ƙwaƙwalwa ta da kuma hujjojin da ke zube a ƙasa, sun nuna min cewa zai yi wahala idan ba na ƙarshe Obi zai zo ba. Ni duk abin da ba zan iya faɗa maka gaba-da-gaba ba, to kuma ba zan faɗa a bayan idon ka ba.
“Saboda haka na faɗa masa ra’ayi na. Babu ma tabbacin Obi ya zo kusa da na biyu ko na uku. Giriftun sa kawai ya ke yi, saboda masu sharhin siyasa sun yi masa romon-kunne, sun ce masa ko babu ginannen tsarin tafiyar siyasa zai iya yin nasara,” inji Obi.
Soludo ya ce a jihar Anambra inda Peter Obi ya fito kaɗai zai iya yin nasara, amma kuma sauran jihohi ko ƙamshin nasara ba zai ji ba.
“Ni idan ya na so ma har kamfen zan iya taya shi. Amma dai banda Anambra babu inda zai iya taɓuka komai.
“Nan ‘yan soshiyal midiya su ka yi ta nuna cewa LP ce za ta lashe zaɓen gwamna a Ekiti da Osun. Da aka yi zaɓe sai LP ta kasa yin wani abin kirki.
“Kuma ni na lura Peter Obi kamar Tinubu ya ke yi wa aikin sharar hanyar yin nasara. Saboda Obi ya zaizaye PDP. Da ni ne har kuɗi zan iya bai wa Obi ya ci gaba da kamfen.”
Peter Obi ya fita daga APGA, duk kuwa da rantsuwar da ya yi a gaban wanda ya kafa jam’iyyar, cewa ba zai taɓa ficewa ba.
Ya taɓa shaida cewa APGA ce jirgin da ya kamata Igbo su shiga ya lula da su kan samun kujerar shugaban ƙasa.
Obi ya fita daga APGA bayan ya yi gwamnan Anambra, ya koma PDP.
Discussion about this post