Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Magashi ya bayyana cewa Najeriya na bukatar addu’o’i ne daga kasar Amurka, ba su rika fiddo sanarwar da zai tada wa ‘yan Najeriya hankali ba.
Magashi ya bayyana wa kwamitin tsaron majalisar dattawa cewa, duk da cewa kwamitin tsaron kasa ya tattauna batun ranar Litinin tare da shugaban Kasa, ba a kyale shi haka kawai ba.
” Idan kaga hayaki, to akwai alamar wuta a wani wuri kenan, saboda ba za mu yi shiru mu dauki abin da wasa ba. Za mu maida hankali kwarai domin ganin wani abu irin abin dake zargi ya auku a babbar birnin kasar dama ko ina a Najeriya.
Daga bisani sai Magashi ya shaida wa kwamitin cewa tuni an umarci ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya gana da mahukuntan Amurka da sauran kasashe domin a rika samun fahimta a tsakanin kasashen.
A taron da aka yi jiya a fadar shugaban Kasa, mai baiwa shugaban Buhari shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ya bayyana cewa sanarwar da Amurka da ta yi ta yi wa ‘yan kasan ta ne da ke zaune a Abuja. Ba gargadi bane da ya sha fi yan Najeriya.
Bayan haka kuma shi kansa babab hafsan tsaron kasa, Lucky Irabor, ya ce dakarun Najeriya na nan a tsaye suna bi kurdi-kurdi, kwararo-kwararo domin dakile duk wani abu da zai iya tasowa.
Discussion about this post