Abu biyu kaɗai idan mutum ya duba da idon basira, zai gane cewa Najeriya ta shiga tsomomuwa a cikin shekaru bakwai. Abu na farko shi ne yadda aka riƙa kukan cewa dala ta yi tsadar da ta ruguza darajar Naira a 2015, bayan an zaɓi Shugaba Muhammadu Buhari, amma ba a kai ga rantsar da shi ba. A wancan lokacin ana canja Dala 1 kan Naira 200 da ɗoriya.
Zaɓen Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya yaƙinin cewa tattalin arzikin Najeriya zai gyaru, ta yadda a cikin ƙanƙanin lokaci darajar Naira za ta farfaɗo. Sai dai kuma tun bayan yawan sa mulki dala ba ta sake sauka ƙasa, sai dai ƙara daraja ta ke yi a Najeriya, yayin da a lokaci ɗaya kuma darajar Naira ke ci gaba da guzanyewa.
A daidai lokacin da aka kafa APC cikin 2014, Dalar Amurka na daidai da ƙasa da Naira 170. Daga cikin alƙawurran da aka riƙa kamfen da su a lokacin, sun ce za su dawo da martabar Naira, ta yadda a duk lokacin da ta yi kokawa da Dala, to ba za ta ƙara shan ƙasa ba.
To sai dai kuma daidai lokacin da Gwamnatin Buhari ta kai shekaru bakwai da rabi kan mulki, a ranar 1 Ga Nuwamba, 2022 an sayar da Dala 1 a kasuwar ‘yan canji (BDC) ta kai har Naira 900.
Ba wani ba ne shugaban mai kula da martabar dala da darajar ta sai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emiefiele.
Emiefiele dai ya karɓi rikon ragamar naira kuma Shugaban Babban Bankin Najeriya bayan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya cire Sanusi Lamiɗo Sanusi.
Emiefiele ne mai sa-ido kan kuɗin Najeriya a lokacin da aka riƙa watandar kuɗaɗen al’umma a’a lokacin mulkin PDP. Shi kan sa Buhari da ya hau mulki, ya taɓa yin iƙirarin cewa lokacin da ake jidar kuɗaɗe kafin PDP ta sauka mulki, Emefiele na da masaniyar waɗanda aka riƙa raba wa kuɗaɗen.
Kai sai da Buhari ya yi rufucin cewa har a kan fallen takarda Emefiele kan yi rubutu ya bayar idan aka ga daga gare shi ne, za a dumbuji kuɗaɗe a bayar kawai.
Bayan an rantsar da Buhari, kaɗan daga cikin abubuwan da ya yi waɗanda ‘yan Najeriya ba su ji daɗin sa ba, shi ne da ya bar Emiefiele ci gaba da rikon CBN. Yayin da a lokacin an yi tittifaƙin cewa tunda Emiefiele ya san ana kwasar kuɗaɗe a lokacin, kuma bai fallasa kamar yadda Sanusi Lamiɗo Sanusi ya fallasa cewa an karkatar da wata Dala biliyan 20, to idan har Buhari bai kama shi an ɗaure ba, to babu dalilin barin sa ci gaba da riƙe CBN.
Ci gaban da Emiefiele ya yi da riƙon CBN bayan Buhari ya sabunta masu ƙarin wa’adin wasu shekaru 5, ya haifar da ka-ce-na-ce, inda jama’a da dama su ka riƙa cewa idan Buhari bai yi taka-tsantsan ba, to sai Emiefiele ya cefa tattalin arzikin Najeriya cikin ragabza. Ai kuwa ga ragabzar nan ana gani, inda yau dala har ta dangana da Naira 900.
Dama Hausawa sun ce duk wanda ya ƙi jin bari, to zai ji hoho. Ba matsalar karyewar darajar Naira kaɗai Emiefiele ya kasa kawarwa ba. Ya na da hannu tsamo-tsawo a tsadar kayan abincin da ake nomawa a ƙasar nan. Saboda Babban Bankin Najeriya ne ke bai wa manoma ramcen maƙudan kuɗaɗen bunƙasa noma. Kuma a duk shekara kayan abincin na ƙara tsada, kuma kuɗaɗe na ƙara lumewa a hannun jama’a.
An ƙirƙiro shirin bunƙasa noman abinci a cikin ƙasa don a karya farashin abinci kuma ya wadata. Maimakon a samu rangwame, a duk shekara sai tsada ya ke ƙara yi. Buhun shinkafar da ake sayarwa Naira 8,500 kafin 2015, a yanzu ya haura naira 30,000. Shinkafar da ake nomawa ɗin nan a cikin gida nema ta ke yi ta gagari talakawa.
Mu dawo kan faɗuwar darajar naira a ƙasar nan? Shin za a ci gaba da dogaro da Emiefiele ya taka mata burkin hana ta ci gaba da lalacewa ne? Idan za a dogara da shi ɗin, ko zai iya? Ko kuwa sa masa ido za a yi har sai ya sauka ko sai wa’adin mulkin Buhari ya cika? Idan aka tafi a haka, to kada a yi mamaki nan da watan Mayu idan Dala 1 ta kai Naira 2,000.
Discussion about this post