Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya, Ado Doguwa ya fallasa wata boyayyar shiri da ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano Sule Garo ke da shi wanda ya haɗa da dagula jam’iyyar APC a Kano.
Da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa a Abuja, Doguwa ya ce, Sule Garu ya faɗi da bakin sa cewa ” Da ya tsaya ya zama mataimakin gwamna a Kano, wanda matsayin sa bai wure ɗan aike ba, gara ya lallaɓa ya bi Atiku, don ya zama sirikin sa.
Doguwa ya kara da cewa Garu ba ta APC ya ke kuma duk abinda zai yi ya yagalgalata a Kano shine ya ke yi.
Daga nan sai ya kara da cewa, ga dukkan alamu APC a Kano na gab da ta zamo gawa, don idan da irin su Garu ne ake tafiya da su, tabbas sai dai kawai a jira yi mata jana’iza bayan NNPP Kwankwaso ta yi dagadaga da ita a zaɓe mai zuwa.
A karshe ya ce, a shirye yake ya koma su ɗinke da Kwankwaso, sai dai kuma ba zai canja sheka ba, yana nan a APC, amma kuma yana tare da Kwankwaso.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin kacamewa da aka yi tsakani Garu da Doguwa a gidan mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna.
Abin dai bai yi daɗi don har fashefashen kounan shan shayi an yi.
Discussion about this post