Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi kamfani da ma’aikatun gwamnati da za su yi aikin hako mai a rijiyar mai na Kolmoni su tabbata sun jawa mutanen yankin a jika sannan sun wadata su da abubuwan mire rayuwa.
Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da shugaban Buhari yayi a wurin kaddamar da rijiyar mai na farko da aka gina a yankin Arewa dake kan iyaka jihohin Bauchi da Gombe.
A wurin kaddamar da wannan rijiyar Ɗanyen mai, Buhari ya ce ” Akwai sama da Ɗanyen mai da ganga biliyan ɗaya, shimfiɗe a kasa sannan kuma da iskar gas ratata a wannan wuri. Tuni gwamnati ta baiwa kamfanin Sterling Global Oil, da kamfanin raya yankin Arewa New Nigeria Development Commission (NNDC) da kuma.kamfanin mai na kasa
NNPC Ltd.
Cikin watan Oktoba, 2019 ne NNPL ta tabbatar da cewa an gano akwai ɗanyen mai da gas a ƙarƙashin ƙasar yankin Kolmani, kuma mai tarin yawan gaske.
Wurin wanda ke da faɗin gaske, ya shafi yankin Upper Benue Basin har zuwa Gongola Basin.
An dai daɗe ana gaganiyar neman ɗanyen man har zuwa cikin Oktoba, 2019 lokacin da aka tabbatar da samun sa.
Buhari ya ce samun ɗanyen man zai bunƙasa tattalin arziki, samar da aiki, samar da kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar mutanen yankin.
Ya ce ya zauna da Gwamnonin Gombe da Bauchi ya umarce su da su sa ido sosai, saboda aikin haƙar ɗanyen mai ɗin ya shafi mazauna yankin.
Discussion about this post