Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya jaddada cewa ba zai taɓa gajiyawa ko daina ƙoƙarin da ya ke yi wajen ganin Najeriya ta zama ƙasaitacciyar ƙasa ba.
Kwankwaso ya ƙara da cewa har kadarorin sa ya riƙa sayarwa don ganin ya ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a jami’o’i daban-daban.
Kwankwaso ya yi wannan bayani a wurin taron murnar zagayowar ranar haihuwar sa da cikar sa shekaru 66 a duniya.
Gidauniyar Ci Gaban Al’umma ta Kwankwasiyya Development Foundation ce ta shirya taron ranar Litinin, a Abuja.
Tsohon Gwamnan Kano ɗin ya ce bayar da ilmi mai inganci shi ne babban jarin da ɗan siyasa zai iya samar wa al’umma. Ya ce shi ya sa ya ke sadaukar da dukiya mai yawa domin ganin cewa ilmi ya yi muhimmin tasiri ga inganta rayuwar jama’a.
Kwankwaso ya ce ɗalibai sama da 3,000 sun ci moriya tare da amfanar shirin sa daga 2011 zuwa 2015 lokacin da ya ke gwamnan Jihar Kano.
Ya ce ya kafa wannan gidauniya ce a matsayin sakayya ga jama’a, saboda irin gagarimin goyon bayan da su ka ba shi lokacin gudanar da zaɓuka daban-daban a jihar Kano.
“Lokacin da mu ka fito da tsarin bayar da gurbin karatu da farko, min kwashe dukkan masu darajar digiri ta farko (first class). Su ma masu digiri mai daraja ta biyu (sencond class) duk mu ka kwashe su.
“Mu na a kan masu digiri mai madaidaiciyar daraja ta biyu (second class lower) ne na bar gwamnati.” Inji Kwankwaso wanda ya kammala wa’adin sa cikin 2015.
“Dalili kenan mu ke da ɗalibai fiye da 3,000 a ƙasashen daban-daban har 14.” Inji Kwankwaso.
Ya ce ‘yan Najeriya da dama sun amfana da gidauniyar ilmi ta Kwankwasiyya matsawar dai a Kano ya ke zaune. Babu ruwan su da nuna bambanci ga wanin da ba ɗan asalin jihar ba, matsawar dai a jihar Kano ya ke zaune.
“Sai da mu ka samu masu Digiri mai daraja ta ɗaya sun kai ɗalibai 400. Mu ka tantance aka ɗauki mutum 370. Ina murna da wannan nasara, domin sun kammala karatun su. Akwai masu aikin nan Najeriya, akwai wasu kuma a ƙasashe daban-daban,” inji Kwankwaso.
A wurin taron dai an yaba da irin mulkin da Kwankwaso ya yi wa Kano, kuma an yi fatan cewa zai yi fiye da haka idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Discussion about this post