Babban Hadimin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Jama’a, Ajuri Ngelale, ya kare mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce masu yawan sukar tulin bashin da ake bin Najeriya su na ƙarin gishiri sosai.
An tattauna da shi a Gidan Talbijin na Channels, a ranar Alhamis.
Ya ce akwai ƙarin gishiri sosai a cikin bayanan tulin bashin Naira tiriliyan 41 da ake cewa ana bin Najeriya.
Buhari ya hau mulki a bisa alƙawarin “CHANJI”, amma kuma sama da shekaru bakwai kenan bayan hawan sa mulki, ba a samu canjin da ake tunanin samu ba, ballantana a ce an cika alƙawarin da aka daukar wa talakawa.
An samu tsadar rayuwa, tashin farashin kayan abinci, kama daga kayan gona har zuwa kayan masarufi.
Akwai matsalar tulin bashi da rugurgujewar darajar Naira.
Kafin saukar PDP daga mulki dai Dalar Amurka ɗaya na daidai da naira 197. Amma a yanzu ta haura 870.
Yayin da bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 41.62, Najeriya ta na biyan kusan ilahirin kuɗaɗen shigar ta wajen biyan basussuka, kuma hatta ma kasafin 2023 sai an ciwo bashin naira tiriliyan 8.2 sannan a iya gudanar da shi.
Kada a manta, bashin da PDP ta sauka ta bari, na naira tiriliyan 12.6 kaɗai.
Duk da haka, Ngelale wanda mataimakin Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Bola Tinubu ne, ya ce APC ta fi PDP ƙoƙartawa, sannan kuma idan mutane su na batun yawan basussukan da Gwamnatin Buhari ta ciwo, ba su yin la’akari da cewa an yi ayyukan raya ƙasa ne waɗanda kowa zai iya gani a fili.
Discussion about this post