Kotun majistare a jihar Kano ta yanke wa Mubarak Isa da Nazifi Bala waɗanda ke shirya gajerun shiri na barkwanci a shafukan sada zumunta hukuncin bulala 20 kowannen su.
Hakan ya biyo bayan karar su da aka shigar ne a makon jiya kan wani bidiyo da suka yi suna ambatar sunan gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, suna karta masa rashin mutunci ta hanyar barkwanci.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan gwamnan da kuma abinda ta ce kokarin tada fitina a cikin al’umma.
Cikin hukuncin da aka yanke wa waɗannan matasa biyu sun haɗa da share harabar kotu na wata guda cur, bayan kuma bulala da za a sharara musu 20-20 kowannen su. Sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin tiktok su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kamar yadda suka irin wancan da ya bata masa suna.
Sai dai kuma su waɗannan matasan ba wannan ne karon farko da suke yin irin haka ba, kai dai tsautsayi nr ya faɗo kan su suka karta wa Ganduje, da shi kuma baya yafiya da gar cewa barkwanci ne kawai, amma dama sukan kwaikwayo muryan manyan mutane ne su haɗa ƴar gajeruwar bidio don nisaɗin masu kallo.
Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, ya gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamna Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina.
Matasan sun amsa laifin su da hakan yasa aka yanke musu waɗannan hukunci.
Lauya mai gabatar da kara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.
Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika wadannan ka’ido kafin a sake.
A nashi ɓangaren, Barista Bashir Yusuf da shi ne lauyan matasan ya gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu kalubalanci hukuncin ba.
Sai dai kuma wasu mazauna garin Kaduna da Kano duk sun yi tir da hukuncin kotun fuk da ko ita kotu aikinta ta aiwatar.
Wani mazaunin Sharaɗa dake jihar Kano, ya ce irin waɗannan bidiyoyi da akan yi na barkwanci ba wani abu bane da zai tada hankalin mutane sai don nishaɗi.
” Ban ga abinda ya yi zafin da za a ce wai har an kai waɗannan matasa kotu ba, kawai don sun yi irin wannan bidiyo na barkwanci. Shi Ganduje da zarar an yi abi komai kankantar sa sai ya sa a kama mutane. Me suka yi na laifi. An yi, kuma har yanzu ana yi wa Buhari, gwamnoni, da sauransu , amma shi nashi a kullum da ban ne. ”
Sadiya Kasim-Bello, Ita ta roki gwamna Ganduje da makarraban sa da su ruka kauda idanun sa ga ireiren waɗannan abubuwa. Abu ne na barkwanci amma sai ace komai ba a so.
Irin waɗannan bidiyo, ba sabon abu bane a Najeriya da duniya baki ɗaya. Akanbyi wa shugaban ni irin wannan barkwanci ta bidiyo, radiyo ko ma a wuraren taro kawai don nishaɗi.
Discussion about this post