Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa kasafin Naira biliyan 21.1 na fadar sun yi kaɗan matuƙa.
Tijjani Umar ya na magana ne dangane da Naira biliyan 7.2 daga cikin kuɗaɗen waɗanda za a kashe a ɓangaren gyare-gyare da kula da fadar.
Kasafin 2023 dai ya ware naira biliyan 21.1 domin kashewa a Fadar Shugaban Ƙasa.
A cikin kuɗaɗen za a kamfaci Naira biliyan biyu a sayo sabbin motoci sannan a kashe naira miliyan 644 wajen gyaran Karamin Ofishin Shugaban Ƙasa da ke Legas.
Najeriya za ta ciwo bashi na sama da tiriliyan 8 kuma za ta biya bashi na sama da tiriliyan 6 duk a cikin 2023.
Ƙasar na fama da matsalar tattalin arziki, ƙarancin kuɗaɗen shiga da kuma tsadar rayuwa.
Najeriya ta ƙara afkawa cikin wani mawuyacin halin da ake canja Dalar Amurka 1 kan Naira 900, alhali lokacin da Buhari ya hau mulki ba ta wuce Naira 200 ba.
Matsalolin Da Su Ka Dabaibaye Kasafin 2023:
Cikin watan Oktoba ne Majalisar Dattawa ta fara zaman nazarin Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20.5, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar Juma’a.
Sanatocin da su ka yi magana da shawarwari a lokacin nazarin kasafin, sun nuna rashin amincewa da yadda Gwamnatin Tarayya za ta kashe har naira tiriliyan 8.2 kan ma’aikatan gwamnati da ayyukan yau da kullum na tafiyar da gwamnati. Amma kuma za a kashe naira tiriliyan 5.35 kacal wajen yi wa ‘yan Najeriya ayyukan raya ƙasa da su ka haɗa har da titina da sauran su.
A kasashin dai Gwamnatin Tarayya za ta ciwo bashin naira tiriliyan 8.27, kuma za ta biya bashin naira tiriliyan 6.31. Sannan kuma ma’aikatan gwamnati za su lashe naira tiriliyan 4.99.
SANATA NDUME: Wauta Ce A Ciwo Bashin Da Za A Kashe Kan Ma’aikatan Da Su Ne Kashi 1% Bisa 100% Na ‘Yan Najeriya:
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa maganar gaskiya bai yiwuwa a ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe naira tiriliyan 8.2 kan ma’aikatan gwamnatin tarayya, waɗanda yawan su bai wuce kashi ɗaya tal na yawan ‘yan Najeriya su miliyan 200 ba.
Ya ce kamata ya yi a ce kuɗin da gwamnati za ta yi wa sauran ‘yan Najeriya aiki ya fi yawan kuɗin da za ta kashe wa ma’aikata fintinkau.
“Amma ai hankali ma ba zai ɗauka ba, a ce wai za a ciwo bashin naira tiriliyan 8.27, kuma a kashe naira tiriliyan 8.2 kan ma’aikatan gwamnatin tarayya. Su kuma sauran ‘yan Najeriya a yi masu aikin naira tiriliyan 5.35 kaɗai.” Inji Ndume.
Daga nan sai ya yi kiran da a binciki yadda a duk shekara kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa kan ta ke ƙaruwa maimakon raguwa, duk kuwa da cewa a kullum fasahar zamani na rage ɗawainiyar kashe kuɗaɗe da kawo sauƙi wajen gudanar da ayyuka.
SANATA BETTY APIAFI: Asusun Gwamnati Na TSA Ya Na Yoyo, A Binciki Waɗanda Su Ka Ɓula Shi:
Sanata Betty Apiafi, wata ‘yar PDP daga Jihar Ribas, ta fallasa cewa akwai rahotannin da su ka tabbatar da cewa Asusun Bai Ɗaya na PDP ya na yoyo, don haka a jingine batun ciwo bashi tukunna, a dawo a yi binciken inda kuɗaɗen Najeriya ke zurarewa, kuma a gano masu tara buhuna su na jide kuɗaɗen.
Ta ce wahalar banza ce duk shekara a yi ta ciwo bashi, amma kuma an kashe toshe hanyoyin da ake kwashe kuɗaɗen ƙasar nan.
SANATA SMART ADEYEMI: Attajiran Da Su Ka Kimshe Kuɗaɗe A Bankuna Su Bai Wa Gwamnati Ramce:
Sanata Smart Adeyemi daga Jihar Kogi, ya bayar da shawarar cewa maimakon a riƙa fita ana ciwo bashi, ya kamata manyan attajiran da su ka kimshe kuɗaɗe a cikin bankuna kuma ba su taɓa kuɗaɗen, su riƙa bai wa gwamnati ramce.
“Akwai maƙudan kuɗaɗe har maƙudan dalolin da manyan ‘yan Najeriya su ka kimshe a bankuna, ba a taɓa su. Ya kamata su riƙa bai wa Najeriya ramce.”
Kaɗan kenan daga cikin waɗanda su ka yi maganganu masu yawa a yayin zaman.
SANATA AHMAD LAWAN: A Daƙile Ɓarayin Ɗanyen Mai Don A Rage Yawan Ciwo Bashi:
Sanata Lawan ya baje faifan yadda Najeriya za ta rage ciwo bashi da rage giɓin kuɗaɗen kasafi
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa matsawar Najeriya ba ta tashi tsaye ta daƙile barayin danyen mai da masu fasa bututu ba, to nan ba da daɗewa ba tattalin arzikin Najeriya zai iya durƙushewa.
Lawan ya yi wannan bayani lokacin da ya ke gabatar da jawabi kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin gabatar da Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20.52 a Majalisar Tarayya.
Lawan ya ce a yanzu ɓarayin ɗanyen mai su ne manyan abokan gabar Najeriya. “Ya kamata a tashi haiƙan a kakkaɓe wannan gagarimar matsalar ta ɓarayin ɗanyen mai, kafin su kai ga tarwatsawa ko durƙusar da tattalin arzikin Najeriya.”
Lawan ya ce idan aka magance gagarimar satar ɗanyen mai, to za a samu ƙarin kuɗaɗen shiga, kuma hakan zai rage ciwo bashi, tare da rage giɓin kasafin kuɗi.
Shawara ta biyu da Sanata Lawan ya bayar, ita ce “a sake nazarin ɗage biyan harajin shigo da wasu kaya da ake yi wa wasu mutane ko kamfanoni. Kuma a rage bai wa wasu kamfanoni iznin karɓar haraji a madadin gwamnatin tarayya ana biyan su lada.
“Kuma a rage bai wa wasu kamfanoni damar kashe kuɗi su na yin wasu ayyukan gwamnatin tarayya, daga baya su na karɓar haraji har sai sun karɓi kuɗin kwangilar su da ribar su tukunna.”
Lawan ya buga misali da cewa hukumomi ne irin su Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hukumar NIMASA da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), duk kamata ya yi su riƙa karɓar harajin su da kan su, kamar yadda Hukumar Kwastan da Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Cikin Gida (FIRS) ke Karɓar na su da kan su, ba wasu kamfanoni ke karɓar masu ba.
Lawan ya ce waɗannan duk hanyoyi ne na ƙarin kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya, waɗanda za su haifar da rage ciwo bashi don a cike giɓi a kasafin kuɗi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Buhari ya ce Za a ciwo bashin naira tiriliyan 8:8, don a cike giɓin Kasafin 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20:51, a gaban Majalisar Tarayya.
Kasafin wanda ya gabatar a ranar Juma’a, shi ne na takwas kuma na ƙarshe a mulkin sa da ya gabatar.
A cikin jawabin sa, Buhari ya bayyana cewa za a samu giɓi na naira tiriliyan 10.78, amma kuma za a cike giɓin da kuɗaɗen bashin da za a ciwo har naira tiriliyan 8.8.
Haka nan kuma ya ce a cikin kasafin, za a kashe naira tiriliyan 6.31 wajen biyan basussuka.
Ya bayyana cewa an tsara kasafin bisa kintacen cewa Gwamantin Tarayya za ta samu kuɗin shiga har naira tiriliyan 16.87 cikin 2023. Kuma ana sa ran a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.69 a kowace rana, yayin da aka yi kintacen cewa za a riƙa sayar da kowace ganga ɗaya kan Dalar Amurka 70.
Wannan kasafin wanda aka raɗa wa suna Kasafin Rage Giɓi Da Rage Ciwo Bashi, ya nuna bai ci sunan sa ba, domin za a ciwo har naira tiriliyan 8.80 a matsayin bashi cikin 2023.
Yayin jawabin sa, Buhari ya yi bitar ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar cikin shekaru bakwai da kuma bibiyar yadda aka kashe kuɗaɗen kasafin 2022.
Discussion about this post