Rundunar Kamfen ɗin ɗan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun maida wa ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, tsohon gwamnan Barno, Kashim Shettima martani.
Idan ba a manta ba, Shettima, ya bayyana Atiku Abubakar da cewa ɗan ci-ranin siyasa ne, kuma za su kayar da shi a 2023, yadda zai koma Dubai inda idon sa ya fi buɗewa ya tare a can.
Shettima ya yi wannan cika-baki yayin da ya ke jawabi wurin taron gabatar wa hamshaƙan masu zuba jari da gaggan ‘yan kasuwa manufofin APC a Legas.
A wurin taron wanda ya gudana ranar Talata, Shettima ya gwasale ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda hatta sai da ya ƙalubalanci takardar shaidar darajar karatun Atiku.
Shettima ya ce, “takardar shaidar da Atiku ya ke tutiya ya mallaka daga ‘School of Hygiene, Kano, ba wata tsiya ba ce, kawai ya fito ne a duba-garin masu kwasar shara.”
Sannan kuma ya yi wa Atiku barkwanci dangane da yadda ya ke yawan fitowa takarar zaɓe amma ya ke yin rashin nasara.
Ya kwatanta Atiku da Raila Odinga na Kenya, wanda ke yawan shiga takarar zaɓen shugaban Kenya, amma ana kayar da shi.
“Ina girmama Atiku Abubakar, amma fa shi shugabanci ya wuce abin soki-burutsu. Takardar shaidar da ya ke tutiya daga ‘School of Hygiene ta Kano, ba wata tsiya ba ce. Matsayin da ya ƙware a can bai wuce duba-garin masu kwasar shara ba.
“Don ka iya sayar da kwalaben ruwan sha, ai wannan ba ƙwarewa ba ce wajen naƙaltar tattalin arziki. Ya zama kamar Raila Odinga na Kenya, wanda ya sha fitowa takarar shugaban ƙasa, amma ya na shan kaye.
“Mu ma a 2023 za mu kayar da shi, ya koma ritayar dole a Dubai, inda ya ke zuwa gallafirin sa,” inji Shettima.
Shettima bai tsaya kan Atiku kaɗai ba. Ya tafka gora kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, wanda ya kira, “almurin da ya iya kintace da shaci-faɗin alƙaluman ƙididdigar tattalin arziki na ƙarya.”
Shettima dai ya ce a cikin dukkan ‘yan takara babu wanda ya kai Bola Tinubu na APC cancanta ya shugabanci Najeriya a 2023.
A cikin martanin wanda Dele Midiya ya fitar, ya bayyana cewa, idan ba zautuwa da dama da cutar mantuwa ba, jam’iyyar APC ta Kashim Shettima ce ke cikin ruɗu da tashin hankali.
” Jam’iyyar APC da ta kasa haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar domin kafa kwamitin kamfen da kowa zai yi na’am da shi, sannan kuma idan ba rudewa ba da rashin sani, har yanzu, wasu da dama daga cikin jigajigan APC suna bin jama’a suna rokon su gafarar taɓargazar da gwamnatin su ta yi, amma yana nan yana wage baki, ta inda ya ke hawa ba ta nan yake sauka ba.
Discussion about this post