Malejin tsadar rayuwa a Najeriya ya ƙara cillawa sama zuwa kashi 21.09 cikin watan Oktoba, 2022. Wannan ke tashin gauron zabi da ya yi sau tara a jere duk wata.
Malejin na tsadar rayuwa ya ƙara yin sama ne daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci, kamar yadda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta bayyana a ranar Talata.
NBS ta yi wannan bayanin a cikin rahoton ta na Jadawalin Alƙaluman Farashin Abinci da Masarufi na watan Oktoba, 2022.
NBS ta ce malejin ya ƙaru ne, domin a cikin watan Satumba, malejin ya na kashi 20.77.
Rahoton na ranar Talata da NBS ta fitar, ta ce a duk wata farashi ƙaruwa ya ke yi har tsawon watanni tara a jere.
NBS ta ce tsadar kayan abinci ya kai har kashi 23.72% a cikin Oktoba, cillawar da ya yi sama daga kashi 23.34% a cikin watan Satumba.
Rahoton ya danganta matsalar tsadar rayuwar da fetur da gas da kuma tsadar kayan masarufi da kayan abinci.
Wanann gagarimar matsala ta shafi Najeriya a daidai lokacin da ake ta fama da ibtila’in ambaliya, wanda ya yi mummunar ɓarnar mamaye garuruwa, kashe mutum 600 da ta kashe.
Discussion about this post