Sanatan Kaduna ta Tsakiya kuma ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a APC Uba Sani, ya yi wa kungiyar kwadagon jihar Kaduna bisharar cewa idan ya zama gwamnan Kaduna zai kula da ma’aikatan jihar Kaduna.
Uba Sani ya kara da cewa ” Ni ma ɗan gwagwarmaya ne, da ni aka rika fafatawa a lokacin mulkin sojoji domin kawo karshen mulkin kamakarya shekaru 30 da suka wuce saboda haka na san matsalolin ma’aikata zan warware su kowa ya wataya.
A karshe shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna, ya Mr Ayuba ya bayyana cewa kungiyar ta yi farin cikin amsa gayyatar su da ɗan takarar yayi kuma nan ba da dadewa ba, za su bayyana ɗan takarar da mambobin kungiyar za su mara wa baya a zaɓen gwamna na jihar.
Discussion about this post