Kwamitin Lura da Kuɗaɗe na Majalisar Wakilai ta Tarayya, ya nuna matuƙar damuwa dangane da ƙwangen kuɗaɗen gudanar da ayyukan da ake yi wa Ofishin Akanta Janar na Ƙasa.
Shugaban Kwamiti Oluwale Oke ne ya yi masu wannan kakkausan zargi ga Ministar Harkokin Kuɗaɗe,. Zainab Ahmed da kuma Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗaɗez Ben Akabueze.
Shugaban Kwamitin ya ce hana Ofishin Akanta Janar isassun kuɗaɗen gudanar da aikin sa, tamkar yi wa yaƙi da cin hanci da Gwamnantin Buhari ke yi zagon-ƙasa.
OK ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da ya ke kare kasafin ofishin sa na 2023 a Majalisar Tarayya.
Akanta Janar ɗin Adolphus Aghughu ne da kan sa ya je kare kasafin.
Ɗan Majalisar ya ce ƙwangen kuɗaɗen da ake yi wa Ofishin Akanta Janar kawai wani ƙullallen tuggu ne domin a gurgunta ƙafafun da Ofishin Akanta Janar ke taƙama ya na yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ɗan Majalisar ya yi fatali da ware wa wani Ofishin Akanta Janar Naira miliyan 62 kacal, domin gudanar da manyan ayyuka, maimakon naira biliyan 2.5 waɗanda kwamitin ya rubuta amincewar a bayar.
Ya ce lamarin rashin mutunci ne kuma abin takaici, a ce a amince za a bayar da naira biliyan 2.5, daga baya a ware wa ofishin Naira miliyan 62 kacal.
“Mun ga irin yadda makusantan Shugaba Buhari, musamman Ministar Harkokin Kuɗaɗe da Shugaban Ofishin Kasafin Kuɗaɗe ke garauniyar yi wa tattalin arzikin ƙasaagon zagon ƙasa.
“Amma idan ba haka ba, ta yaya za su narka biliyoyin kuɗaɗe a cibiyoyin da ba wani ƙwaƙƙwaran tasiri gare su ba, shi kuma Ofishin Akanta Janar sukutum a ware masa Naira miliyan 62.”
“Ofishin Kasafin Kuɗi ya karya doka, saboda ya kamfaci kuɗi ya ba cibiyoyin da ba su komai, a waje ɗaya kuma ya bai wa Ofishin Akanta Janar a ba shi naira miliyan 62 kacal.
Discussion about this post