• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

Ku Guji Auren Dole Domin Zaman Lafiyar Al’ummah! Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
November 4, 2022
in Ra'ayi
0
Two Women

Two Women

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwana masu albarka, ku sani, wallahi auren dole bala’i ne, fitina ne, musiba ne, hadari ne kuma addinin Musulunci ya hana shi. Don haka idan muna son zaman lafiya, idan muna son kubuta da tsira anan duniya da kuma lahira, wallahi sai mun guji abunda addinin mu ya hane mu!

Ya ku al’ummah! Ku sani, auren dole shine a aurawa mace ko namiji matar da ko mijin da dayan ma’aurata baya so. Irin wannan auren sanannen abu ne a tsakanin wannan al’ummah ta mu, kuma illarsa sananniya ce. Dan uwa auren dole yana da fuskoki da yawa, ko dai mijin ya nace sai ya aura, kuma yasan matar bata son shi, ko kuma iyaye su nace sai sun aurar ga wane, alhali sun san ‘yar tasu bata so, ko kuma matar ta nace sai ta auri wane, alhali ta san ba ya son ta. Tabbas duk wadannan sigogin auren zasu shiga cikin auren dole, kuma illarsa a fili take ga kowa da kowa.

Manufar aure mafi girma ita ce samun natsuwa da kwanciyar ga namiji daga matarsa, haka ita ma ta samu natsuwa da kwanciyar hankali daga mijinta, kuma ya zamanto sun amfani juna ta hanyar samun ladar junansu, a matsayinsu na miji da mata. Irin wannan manufa ba’a samunta a auren dole, don kuwa bakin ciki ake samu maimakon farin cikin da zai kawo natsuwa.

Ya ‘yan uwa masu daraja! Wallahi akwai mamaki, ace mace bata son ka amma ka matsa sai ka aureta, kuma kayi ta bin hanyoyi iri-iri, daban-daban na ganin kayi nasara akan ta, alhali kasan ba ta son ka. Dan uwa ka bar baiwar Allah tayi aure irin na soyayya. Mafi girman matsala ga mace shine kuskurewa akan zabin miji. Idan bata son ka to kayi mata fatar alheri, ka je ka nemi wadda ta ke son ka, wannan shine zaman lafiya da samun natsuwa bayan aure daga matar da kake aure. Haka ma za ka ga namiji bai son mace amma tana ta kokarin sai ta aure shi, bata san cewa zaman lafiya ga mace yana wurin samun miji mai son ta ba. Malam don Allah, kar ka auri wadda bata son ka, ke ma don Allah kar ki auri wanda ba ya son ki. Soyayya ginshiki ne mai girma a cikin zaman aure, sannan samun farin ciki yana ga masoya.

Ya ku iyaye! Ku sani, wallahi kune mafi girman abun zargi akan auren dole, domin mafi yawa mata ake yiwa auren dole. Sannan kuma ga Shari’a, su mata basu aurar da kansu, sai dai iyayensu su aurar dasu ko wakilan iyayen. Don haka dan uwa shin meye ribarka na yiwa ‘yar ka auren dole? Shin baka san ka jefa ta cikin kuncin rayuwa bane na har abada? Shin baka san kamar kace ta je ta karar da rayuwarta ne cikin bakin ciki da damuwa ba? Shin baka san cewa yi mata auren dole zai sa ta gagara yin biyayya ga mijin da ka aura mata ba? Shin baka san rashin biyayya ga mijin da ka aura mata zai sa ta fada cikin fushin ubangijin ta ba? Koma dai mene ne, kasan da sanin kai ne dalilin da yasa ‘yar ka ta fada cikin duk wannan halin ko?

Don Allah meye ribarka na kayi mata auren dole? Wanda a sanadin haka kuna iya kunyata, da kai da ita tun anan duniya, domin kuwa kiyayyar da ta ke yiwa mijin da ka aura mata zai iya kai ta ga daukar mataki, har na raba shi da rayuwarsa, kamar yadda muke ji kuma muke ganin yana faruwa cikin wannan al’ummah, wanda hakan zai sa har kai mahaifin, ka karar da rayuwarka cikin kunci da nadama.

Don Allah idan mace bata son mutum kar ku damu da cewa mai dukiya ne ko mai addini ne ko kuma dan gidan wanene, kar wannan ya dame ku, kar wannan ya rude ku, in har ta kawo wanda take so, to ku bata shi, matukar mai addini ne kuma kun yarda da dabi’unsa da halayensa, kamar yadda Annabi (SAW) ya umurce mu, yin hakan shine mafita da maslaha gare ku da kuma ita ‘yar ta ku.

Shin dan uwa ko kasan da cewa Shari’ar Musulunci bata amince da auren dole ba? Lallai Shari’a bata son auren dole kuma bata maraba da shi. Wallahi mace takan iya rayuwa har mutuwar ta, ba tare da ta canza ra’ayinta akan wanda bata so ba, sai ‘yan kadan daga cikin su, gwargwadon kyautatawar wanda suka aura din.

Da yawa auren dole ya kan jawo fandarewar yara ga iyayensu, kuma ya kan jefa wasu cikin dabi’ar ha’intar mazajensu. Za ka ga mace da aurenta, amma ta gagara rabuwa da tsohon saurayinta, kuma har tarayyar ta kan kai su ga aikata fasikanci, alhali tana da auren wani akan ta. Auren dole ya kan sa haka, kuma jama’ah sun san da hakan, sai dai ke baiwar Allah, ki sani, hakan ba uzuri ba ne a gare ki wurin Allah na aikata fasikanci, wai don an yi maki auren dole. Dole ne ki yarda da kaddara, kiyi hakuri, ki rike amanar mijinki, kuma ki rike tarbiyyar iyayenki.

Kuskure ne a gare ki babba, kuma tozarta ibadar aure ce da ‘ya’yanki da zaki haifa. Ci gaba da hulda da tsohon saurayinki don an yi maki auren dole, ‘yar uwa kar ki kuskura kiyi wannan kuskuren.

Iyaye a kiyaye a tabbatar an aurar da ‘ya’ya ga mazaje na kwarai, masu addini da dabi’u ta kwarai, tare da samar da soyayya tsakaninsu. Idan kun fahimci shi ya dace da ita, sai kuyi kokarin cusa mata sonsa, ba wai da karfi da yaji sai wanda kuke so ba. Kuma tun farko ka tabbatar kayi wa ‘yar ka tarbiyyah irin wadda za ka iya zaba mata miji kuma a zauna lafiya, ba kabar kowa yaje kan ta, ba izinin ka ba.

Yana daga cikin illolin auren dole irin yadda rundunar ‘yan sandan jihar Borno, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda Abdullahi Umar ta ruwaito wani labari ranar lahadi, 30 ga watan Oktoba 2022, na kama wata matar aure ‘yar shekara 25 mai suna Fatima Abubakar, bisa zargin kashe mijinta, Goni Abbah da guba. Mijin nata wanda yake malami ne kuma limami, ya dawo Masallaci, ta bashi abincin sa, ashe ta zuba masa guba yaci, nan take aka garzaya da shi zuwa asibitin kwararru na jihar Borno, inda aka ba shi kulawar gaggawa (emergency), amma abin takaici, daga baya ya rasu bayan sun dawo gida.

Matar da ake zargin ta amsa laifin da ake zargin ta da shi, inda tace ta sayi gubar ne a kasuwar Monday Market da ke cikin birnin Maiduguri, a lokacin da ta riga ta yanke shawarar kashe shi. Tace ta kashe mijinta ne da guba saboda ba ta son shi.

Tace an tilasta mata ta aure shi, alhali ita kuma bata son auren; tace kuma kullun idan ta gudu ta tafi gida wurin iyayen ta, sai iyayen su tilasta mata, su mayar da ita gidan sa!

Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah, Ya Allah ka hada mu da wadanda muke so, suke son mu. Ya Allah ka zabar wa ‘ya’yan mu mazaje na kwarai, su kuma mazan ka basu mata na kwarai masu son su, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Alhamis, 03/11/2022. 08038289761.

Tags: AbujaAureHausaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

YAƘI DA FATAKEN MUGGAN ƘWAYOYI: NDLEA na buƙatar ƙarin karnukan sinsino hodar Ibilis – Buba Marwa

Next Post

MASU LAYYA SU NA HIDIMA DA NAMA: Kasafin Naira biliyan 7.2 na gyare-gyaren Fadar Shugaban Ƙasa sun yi kaɗan – Umar

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Mun cika alƙawuran da muka ɗauka wa ƴan Najeriya – Buhari

MASU LAYYA SU NA HIDIMA DA NAMA: Kasafin Naira biliyan 7.2 na gyare-gyaren Fadar Shugaban Ƙasa sun yi kaɗan - Umar

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda bashin da Chana ta hana Najeriya ya kawo cikas a noman shinkafa, da aikin titin jirgin ƙasan Ibadan zuwa Kano
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: ‘Ban so Najeriya ta afka cikin raɗaɗin ƙuncin da ake fama da shi ba’ – Tinubu
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: ‘Za yi wa masu ƙaramin albashi ƙarin Naira 25,000 tsawon watanni 6 a jere
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: Fassarar Jawabin Shugaba Tinubu:
  • SHARI’A A KOTUN AMURKA: Atiku ya kada Tinubu, kotu ta umarci Jami’ar Chicago ta damƙa wa Atiku kwafen takardun bayanan Tinubu

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.