A ranar Litinin ce Babbar Kotun Tarayya ta ƙwace jimillar naira miliyan 775 da wasu gidaje uku daga tsohon Akanta Janar na Tarayya, Jonah Otunla da Bello Fadile.
Shi kuma Fadile tsohon hadimin Sambo Dasuƙi ne, lokacin ya na wa Shugaban Ƙasa Mashawarcin Harkokin Tsaro.
Wasu daga cikin kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da Lamba 8, Ajayi Crowther Street, Asokoro, Abuja, fili a Cadestral Zone, lamba 1960, A05, Maitama, Abuja.
Hukumar EFCC ce ta fitar da sanarwar kame kadarorin a ranar Litinin.
Sauran kuma otal ne a ke kan ginin sa, a fili mai lamba 621, Titin 37, Gwarimpa, FCT Abuja da wani gida mai ɗaki 4 7th Avenue, Gwarimpa, Abuja.
Haka Kakakin EFCC Wilson Uwujaren ya bayyana cewa Mai Shari’a D.U Okorowo ne ya yanke wannan hukunci.
Uwujaren ya ce EFCC ta ce kotu ta gamsu da cewa an gina gidajen da kuɗaɗen sata da harƙalla.
Mai Shari’a Okorowo ya bayar da umarnin ƙwace kadarorin da kuɗaɗen baki ɗaya, bayan EFCC ta shigar da ƙarar neman a ƙwace dukiyoyin.
Lauyan EFCC Christopher Mshelia ya shaida wa kotu cewa ta gaggauta ƙwace dukiyoyin da kuɗaɗen faufaufau.
Ya shaida wa kotu cewa kuɗaɗen da su Bello Fadile da Jonah Otunla su ka sayi kadarorin da su, EFCC ta yi bincike ta gano cewa kuɗaɗen harƙallar kwangila ne a ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, wato Sambo Dasuƙi, lokacin ya na kan mukamin.
“Shi kuma Otunla da Otunba Ade Adelakun sun maida naira miliyan 775.”
Idan za a iya tunawa, shi ma Akanta Janar Ahmed Idris wanda ya gaji Otunla, an kama shi da zargin wawurar Naira biliyan 109.
Discussion about this post