Wani kurtu da tuni na tsare a hannun rundunar sojin kasa ya kashe Birgediya Janar O.A. James a barikin sojoji dake Abuja ranar Talata.
Majiya ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa wannan kurtu dai ya fito ne daga gidan giya bayan yayi mankas dinsa sannan ya shiga motarsa ya rika tangale tangale da ita a bariki a daidai Janar James ya na tafiyar sa salin-Alin za shi gidan sa dake cikin bariki.
” Da farko mun hango wannan Soja cikin motarsa a guje yana ta tangal-tangal ya wuce mu, daga nan ne muka ji kwatsass ya daki wani abu. Ashe Birgediya Janar James ne ya buge. Ko da aka suntumeshi zuwa asibiti, likitoci nan take suka ce ya rasu.
Rundunar Sojoji ta tsare wannan kurtu zuwa a kammala bincike akan abinda ya faru.
Janar James, babban soja ne dake aiki a sashen kudi na rundunar Sojin Najeriya.
Discussion about this post